Boko Haram: Mutum uku sun mutu yayin hare-haren da aka kai birnin Maiduguri

An wallafa

An kai wa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin tarayyar Najeriya hare-hare inda aka tayar da abubuwa masu fashewa kamar yadda waɗanda suka shaida lamarin suka tabbatar.

Ma'aikatan lafiya da suka isa wurin sun ce mutum uku sun rasa rayukansu kuma shida sun jikkata.

Mazauna birnin na tsakiyar shirye-shiryen bukukwan sallah babba ne yayin da lamarin ya auku.

An sami rahotannin fashewar wasu abubuwan da ake kyautata zaton bama-bamai ne a cikin birnin da yammacin Alhamis.

Shugaban sashen samar da tsaro na hukumar bayar da agaji ta Jihar Borno, Bello Ɗambatta ya ce an harbo wasu gurneti guda huɗu daga wajen birnin, inda suka faɗa wurare daban-daban.

Mohammed Abubakar wanda ya gane wa idonsa lamarin ya shaida wa BBC cewa gurnetin sun fashe ne a wasu yankunan birnin da ke cike da jama'a daura da ofishin jami'an shige-da-fice a lokacin da 'ƴan kasuwa da mazauna birnin ke komawa gidajensu.

A ƴan shekarun nan, mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare yankunan da ke gefen birnin, amma ba kasafai su kan kai hari cikin birnin ba.