Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An fara aikin Hajji da maniyyata ƙalilan a Arafat
An fara aikin Hajji na shekarar Musulunci 1441, kuma Musulmin duniya sun hallara a Saudiyya sai dai ba su da yawa saboda kiyaye kamuwa da cutar korona.
An dai hana alhazai daga ƙasashen waje zuwa Makkah domin yin aikin Hajjin a bana cikin wani ƙoƙari da mahukuntan ƙasar ke yi na hana cutar ƙara bazuwa.
Maniyyata 10,000 ne ake sa ran za su yi aikin Hajjin, ƙasa da kimanin miliyan biyun da aka saba gani.
Ilahirin maniyyatan dag ƙasashen waje suke zuwa aikin ibadan, amma a bana an kyale ƴan ƙasashe wajen da ke zaune cikin ƙasar ne kawai su tafi Makkah domin yin daya daga cikin ayyukan ibada biyar mafi muhimmanci ga Musulmin duniya.
Mene ne aikin Hajji?
Zuwa Makkah domin yin aikin Hajji a kalla cikin rayuwar Musulmi na cikin shikashikan Musulunci biyar - shilashikan da kowane Musulmi da ke cikin ƙoshin lafiya, wanda kuma ke da halin zuwa ake buƙatar ya tabbata ya sauke nauyin da addinin Musulunci ya ɗora kansa.
A birnin Makkah maniyyacin zai halarci masallacin Ka'aba wanda shi ne masallacin da yafi kowane wurin ibada daraja a faɗin duniya ga Musulmi inda za su riƙayin ayyukan ibda kamr ɗawafi da addu'o'i.