A cikin jaka na soma gudanar da sana’ata'

Joselyne Umutoniwase

Asalin hoton, Jeroen Van Loon

Bayanan hoto, A 2018 ɗaya daga cikin babban burin Joselyne Umutoniwase ya tabbata lokacin da aka gayyace ta bikin bajekolin kayan ƙawa a Milan
    • Marubuci, Daga Andrea Dijkstra
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Kasuwanci a Kigali, Rwanda
  • An wallafa

Shirin BBC na mako-mako mai taken The Boss yana duba rayuwar 'yan kasuwa daga sassa daban-daban na duniya. A wannan makon mun yi hira da wata mai yin kayan ƙawa 'yar Rwanda Joselyne Umutoniwase.

A shekarar 2010, Joselyne Umutoniwase ta ɗauki wani muhimmin mataki na rayuwarta. Ta shafe shekara biyar tana aiki a matsayin mai tace fina-finai amma sai ta yanke shawarar cika burinta na zama mai ɗinka kayan ƙawa.

Ta fara wannan sana'a ne lokacin da ta yi tafiya daga Rwanda zuwa Jamus domin wani tallafin karatu kan fim inda ta tafi da wasu akwatuna biyu cike da riguna da sket-sket.

"Matasa a Jamus sun yi sha'awar salon kwalliyar da kuma kalolin da ke jikin atamfofin," a cewarta.

Ta ce ta sayar da waɗan nan kaya ne cikin wata uku.

"Ban san cewa zan iya samun kuɗi sosai ba ta hanyar sayar da kayan sawar dana ke ɗinkawa ba," a cewarta daga wurin sana'arta .

fashion

Asalin hoton, Jeroen Van Loon

Irin kwarewar da ta samu a Jamus ya ba ta ƙwarin gwiwa tare da buɗe mata hanyar samun kuɗi da ya sauya ta daga mai tace fina-finai zuwa masi ɗinka kayan ƙawa.

Ta dakatar da aiki a matsayin mai tace fina-finai inda ta sayi keken ɗinki guda uku, ta yi hayar masu ɗinki sannan ta kafa na ta kamfanin da ta yi wa laƙabi Rwanda Clothing.

Yanzu, bayan shekara takwas, tana da shago ɗauke da masu ɗinki har 37 kuma tana sayar da kayayyakin ne daga $50 zuwa $120.

Tufafi dai na matuƙar burge Joselyne a lokacin da take tasowa a Rwanda.

clothes

Asalin hoton, Jeroen Van Loon

Bayanan hoto, "Ban san cewa zan iya samun kuɗi sosai ba ta hanyar sayar da kayan sawar dana ke ɗinkawa ba," a cewarta

Tana sayen gwanjo masu sauƙin kuɗi da mutane ba sa shawa, kamar yadda ta faɗa. "Ina farke ɗinkin da aka yi wa kayan domin ganin yadda aka ɗinka."

Amma da yadda ake iya shigo da kayayyaki daga China da India zuwa Rwanda, ba ta yi wa abin kallo a matsayin aikin yi ba, a maimakon haka, sai ta karanci harkar fina-finai da kuma ɓangaren fasaha domin ta faranta wa iyayenta rai.

Mahaifinta da kawunta duk suna da sana'oinsu. Hakan ya ƙara mata ƙwarin gwiwar fara sana'ar kitso a lokacin da take kwaleji.

Sai dai irin abubuwan da mahaifinta da kawun nata suka fuskanta ya sake tabbatar mata cewa ba kullum ake kwana a gado ba. "Na fuskanci takaici ina yarinya, lokacin da mahaifina ya daina sana'ar fawa saboda abokin kasuwancinsa ya gudu da kuɗaɗensa."

cloth cutting

Asalin hoton, Jeroen Van Loon

Bayanan hoto, Joselyne tana da shago da maɗinka 37 da suke aiki ƙarƙashinta

Samun kuɗi ma wani babban ƙalubale ne a wajen Joselyne saboda bankuna ba sa son bai wa masu irin sana'arta rance.

"Ƙawa abu ne da ba a ɗauke shi da mahimmanci ba a lokacin," a cewarta kuma a wajen bankunan, "kasancewa ta 'yar shekara 24 data ke da kamfanin kanta bai zama hujjar ba ta bashi ba."

Sai dai ta haɗu da wani lauya kuma mai hannun jari Roman Schulz lokacin da ta je Jamus a 2010. Ya ji daɗin ganin ayyukanta da kuma fasahar da take da ita wajen haɗa kayan ƙawa kuma ya ksance mijinta kuma abokin kasuwancinta.

Sun yi amfani da ajiyarsu ta $10,000 wajen ɗauko ma'aikata na farko.

Ta amince da cewa ta yi kuskure a wasu lokutan, Misali, a wasu bukukuwan nuna kayan ƙawa da ta halarta.

"Wannan ya yi kyau kuma yana da mahimmanci amma ba lalle ne ina buƙatar masu sa kayan ƙawa 25 ba a kan dandali sannan na gayyaci manyan baƙi. Da zan iya yin hakan cikin sauƙi ba tare da na kashe kuɗaɗe masu yawa ba," kamar yadda ta ce.

store

Asalin hoton, Jeroen Van Loon

Bayanan hoto, Samun kuɗi ma wani babban ƙalubale ne a wajen Joselyne saboda bankuna ba sa son bai wa masu irin sana'arta rance.

"Dama Joselyne tana da burin sana'a," a cewar Alice Nkulikiyinka, shugabar Ƙungiyar kwararrun 'yan kasuwa a Rwanda.

"Kamfaninta ya samu ci gaba inda yake samar wa sama da mutum 40 aikin yi. Joselyne ta kafa kamfanin ƙawa da ya yi fice a duniya.

A 2018 ɗaya daga cikin babban burin Joselyne Umutoniwase ya tabbata lokacin da aka gayyace ta bikin bajekolin kayan ƙawa a Milan.

"Babbar nasara ce kasancewa ta a wajen, a cewarta. Ta ce za ta so fara sayar da kayayyakinta ga duniya ta intanet amma tana fuskantar ƙalubale.

clothes

Asalin hoton, Jeroen Van Loon

Bayanan hoto, "Matasa a Jamus sun yi sha'awar salon kwalliyar da kuma kalolin da ke jikin atamfofin," a cewarta.

A yanzu tana ƙoƙarin buɗe shago ta intanet a Turai na sayar da matashi da ɗankwalaye da kuma jakunkuna. Amma tana son ta yi haka ne ba tare da ta manta da kwastamominta na farko ba.

"Idan ka samu ci gaba a ɗan ƙanƙanin lokaci sannan ka daina yi wa kwastamominka abin da suke so, za ka iya rusa sana'arka."

Amma annobar korona ta dakatar mata da wannan ƙudiri.

"A kan dole muka rufe shagonmu lokacin da aka yi dokar kulle ta tsawon kwana 45. Kuma duk da gwamnati ta sassauta dokar a baya-bayan nan, har yanzu babu kwastamomi kamar da."

Presentational grey line

Masu yi mata ɗinka na aiki a lokuta daban-daban domin bin shawarar ba da tazara, a cewarta.

"A Rwanda, mun saba da ƙalubale. Hakan yana sa mutum ya ƙara yi wani abin bajinta, ya koyi yadda zai warware matsaloli sannan ya samu wasu sabbin dabaru."

Joselyne da iyalinta sun gujewa yaƙin basasa a Rwanda a shekarar 1994 inda ta rasa kakanninta da wasu yayyen mahaifanta da kuma 'yan uwa.

Ta ce lamarin ya faru ne a lokacin tana 'yar shekara shida.

shop

Asalin hoton, Jeroen Van Loon

Tun da farko, ta so barin Rwanda baki ɗaya.

"Abin takaici ne a ce irin haka zai iya faruwa a ƙasata kuma ina tsoron hakan na iya sake faruwa.

"Amma za ta kai wani lokacin da za ka haƙura. Duk ma abin da kayi, ba za ka iya gyara lamarin ba.

"Na kuma ga sabbin tituna da ake yi, da sabbin gidaje da ake ginawa. Na ga ana kawo sauyi a ƙasar. Kuma abin daɗin shi ne bayan tashin hankalin, har yanzu mutane na ci gaba da rayuwarsu a wajen."