Hajj 2020: Abubuwa biyar da suka kamata a sani game da Ranar Arafat

Mahajjata

Asalin hoton, KARIM SAHIB

An wallafa

Ranar Arafa, ita ce ranar 9 ga watan Zul-Hijjah na kowace shekarar Hijira.

A cikin wannan rana ce Alhazai a kowace shekara ke taruwa a filin Arafat da ke garin Makkah tun bayan kaucewar rana daga tsakiyar sama zuwa faduwarta don gudanar da daya daga cikin rukunan aikin Hajji.

Mun tattauna da wani malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr Ibrahim Disina, kan abubuwan da suka kamata a yi a wannan rana mai muhimmanci.

Abubuwa biyar cikin falalar wannan rana sun hada da:

1. A irin wannan rana ce lokacin Hajin Ban Kwana a zamanin Annabi Muhammad (S.A.W), Allah ya kammala saukar da hukunce-hukuncen Musulunci, domin tun wannan rana ba a kara saukar da wani hukunci ba.

Wannan ya sa Sayyidina Umar ya ce: "Muhimmacin wannan rana, in da Yahudawa ne da sun dauke ta ranar biki kowace shekara", kamar yadda bayan wannan rana da kwana 81 Allah ya karbi rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

2. Yin Addu'a yayin tsayuwar Arafa ita ce mafi tsada da daraja cikin duk wata addu'a a duniya, kamar yadda Annabi (S.A.W)) ya ce: "Mafificiyar addu'a ita ce addu'ar Ranar Arafa."

Wannan layi ne

3. A ranar Arafa ne Allah ke yawaita 'yanta mutane daga shiga wuta. Hakan ya zo cikin abin da Imam Muslim ya rawaito cewa: "Annabi (S.A.W) ya ce: 'Babu wata rana da Allah ke yawaita 'yanta mutane daga wuta kamar Ranar Arafa"

4. Azumi Ranar Arafa yana kankare zunuban shekara biyu, kamar yadda Annabi (S.A.W) ya ce: "Azumin Ranar Arafa yana kankare zunubin shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa," Muslim ya rawaito hakan.

5. Allah yana alfahari da Alhazai mahalarta Arafa cikin wannan yinin, Imamu Ahmad ya rawaito cewa: "Annabi Sallahu alaihi wasallam ya ce: 'Allah yana alfahari da mazauna sama da wadanda suka halarci filin Arafa.'"