Gwamnatin Jihar Sokoto za ta shuka bishiya miliyan biyu

Asalin hoton, @AWTambuwal
Kwamishinan Muhalli na Jihar Sokoto, Alhaji Sagir Bafarawa ya ce gwamnatin jihar na shirin shuka bishiya miliyan biyu.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a ƙauyen Gangan na Ƙaramar Hukumar Shagari ranar Asabar, yayin da yake ƙaddamar da shirin shuka bishiya 6,000 da wata ƙungiya mai zaman kanta za ta yi.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya wallafa hotunansa yayin da yake ƙaddamar da shirin shuka bishiyoyin ranar Laraba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
"Wannan abin a yaba ne kuma wanda zai taimaka wa yunƙurin gwamnati na shuka bishiya miliyan biyu domin tallafa wa muhalli," in ji kwamishinan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.
Ya ƙara da cewa shuka bishiyoyi zai ci gaba da kasancewa manufar gwamnatin Jihar Sokoto, wanda da ma yake da ɗumbin tarihi.
Sannan ya buƙaci jama'a da su taimaka wurin samun nasarar shirin.






