Hotunan Afirka na wannan makon daga 10 - 16 Yuli 2020

An wallafa

Zababbun kayatattun hotuna daga sassan Afirka na wannan makon:

Tambarin hannu a jikin bangon koko

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tambarin hannu a kokon Munjiriri da a baya ake zuwa bauta a Maasai, an ga wannan tambarin ne a ranar Laraba a Kenya
Mutum-mutumin da aka yi da tagula amma aka file kan sa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Hoton wani mutum-mutumi a Burtaniya da aka cirewa kai sakamakon adawar da masu fafutika suka nuna kan zanen da ke nuna mulkin mulaka'u a kan Afirka. An dauki wannan hoton ranar Laraba a Cape Town.
Wasu mutane kenan da suka juya baya sakamakon tekun da ke tumbatsa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A dai birnin Cape Town din, wannan wasu baki ne wasa da ruwa a bakin teku a ranar Litinin sakamakon tumbatsar da ruwan ke yi
Atamfofi jere a wani shagon sayayya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Tufafi da atamfofi jere a wani shagon sayar da atamfofi da ke birnin Monrovia na Liberia. An dau wannan hoton ne ranar Litinin bayan sassauta dokar kulle da sake bude harkokin kasuwanci.
Mutane Uku na kokarin ceto dan gwagon-birin a wani daji

Asalin hoton, Wales News Service

Bayanan hoto, Likitan dabobbi da masu kula da dawa na kokarin cire kibiyar da masu fatauci suka harba kan dan gwaggon-biri a gidan adana namun daji Virunga da ke Jamhuriyar Demokradiyar Congo.
Rosewood

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Itatuwan madubiya a kusa da bakin kogin Kamakwie a Saliyo ranar Lahadi. Bukatar itacen da China ke yi ya asasa fasakwaurinsa a nan da wasu yankunan yammacin Afirka a shekarun baya-baya nan
Wata mata tsaye tana baiwa shukoki ruwa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Emma Charqui na bai wa shukokinta ruwa a gidanta da ke Tunis ranar Laraba. Matashiyar mai shekara 27 an tura ta gidan yari na tsawon wata shida, bayan ta wallafa wasu sakonnin Facebook da rubutun da ke kama da ayoyin Kur'ani
Wani mutum tsaye a wajen Masallaci

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Taron mutane a masallacin Bamako a ranar Lahadi inda manyan malamai da jagoran 'yan adawa Mahmoud Dikko suka jagoranci addu'o'i ga mutane da suka mutu a rikici da jami'an tsaro.
Wata mata na wucewa ta inda aka sanya alamomin bai wa juna tazara a Nairobi a ranar Laraba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mata na wucewa ta inda aka sanya alamomin bai wa juna tazara a Nairobi a ranar Laraba.
Wata Fasinja sanye da takunkumin fuska

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hakazalika a Nairobi, a ranar Litinin wata fasinja zaune a jikin jirgin kasa da ke zuwa birni na biyu mafi girma a kasar Mombasa

Hotuna daga AFP, Getty Images, EPA da kuma Reuters.