Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tasirin Coronavirus: Mutum 74,000 sun mutu a Indiya, miliyan biyu sun kamu a Brazil
Mutum fiye da 74,000 sun mutu a Brazil kuma alamu na nuna cewa adadin ya fi haka.
Mutum fiye da miliyan biyu ne suka kamu da cutar ta korona kuma babu wata alama da ke nuna cewa adadin zai ragu nan kusa.
Ƙasa da wata ɗaya kenan da aka tabbtar da samun mutum miliyan ɗaya da suka kamiu da cutar a ƙasar.
Brazil da ke da mutane kusan miliyan 210, ita ce ƙasa ta biyu da cutar ta fi yi wa illa bayan Amurka.
Sai dai Shugaban Ƙasar Jair Bolsonaro, wanda shi ma ya kamu da cutar, na ci gaba da nuna cewa cutar ba ta da wani tasiri kuma ya riƙa rashin goyon bayan dokokin yin nesa-nesa da juna.
A Indiya kuwa, tuni waɗanda suka kamu da cutar suka zarta miliyan ɗaya, inda aka samu mutum kusan 30,000 da suka kamu a ranar Alhamis, a cewar rahoton kafar yaɗa labaran ƙasar.
Duk da yake Indiya ta sanar da mutum na farko da ya kamu da cutar cikin watan Janairu ne, annobar ta shiga cikin ƙasar ne sannu a hankali.
Wasu na ganin hanzarin da gwanatin ƙasar ta yi na kulle kasar, ciki har da hana jirage daga ƙasashen waje sauka a ƙasar ya taimaka.
Ƙwararru na ganin wasu jihohin har da birnin Delhi sun yi sakacin ɗaukar mataki, shi ya sa alƙaluman amsu cutar ke ƙaruwa.
Jihar Maharashtra da ke yammacin ƙasar ne cibiya mafi girma ta masu cutar korona - akwai fiye da mutum 280,000 a halin yanzu - kuma ita ce kan gaba tsakanin dukkan jihohin kasar.
Amma akwai wasu wuraren da cutar ke ƙara haɓaka cikin jihohin kudancin ƙasar - ciki har da Karnataka da Andhra Pradesh - a gabashin ƙasar kuma - Bihar da West Bengal.
Su ma sun killace al'umominsu a gida - kwanan nan mazauna birnin Chennai (Madras) na kudancin ƙasar su ka fito daga kulle, kuma mazauna Bangalore, wadda shi ma ke kudancin ƙasar na tsakiyar kullen mako guda.
A 'yan watannin nan ana ta samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar, wadda ke da adadi na uku mafi yawa a duniya bayan Amurika da Brazil.