Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fahim Saleh: An gano gawar mai kamfanin Gokada a New York
Ƴan sandan New York sun sanar da cewa an kashe Fahim Saleh, mai kamfanin Gokada a wani gida da ke Manhattan na birnin.
Wakilin BBC Kunle Falayi ya ruwaito cewa ƴar uwar Mista Saleh ce ta gano gawarsa ranar Talata.
Kakakin Ƴan Sandan na New York ya ce bayan an kashe shi, an kuma daddatsa gawarsa da wani zarto mai amfani da lantarki wanda ƴan sandan suka taras a kusa da gawar mamacin.
Mista Saleh ya kafa kamfanin Gokada - kamfanin da ke samar da baburan haya a Najeriya cikin birnin Legas a 2018 - wanda ya kawo sauyi ta fuskar fasahar zamani ga harkar sufuri a babban birnin kasuwancin Najeriya.
Jarin kamfanin ya kai dala miliyan 5.3 a lokacin da ya fara aiki cikin watan Yunin 2019.
Kamfaninsa ya sanar da kisan da aka yi wa ɗan kasuwan a Twitter, kuma labarin ya girgiza ƴan kasuwa masu yawa - musamman na bangaren fasahar sadarwa.
A watan Fabrairun 2020, Mista Saleh ya mayar da kakkausan martani cikin wani bidiyo da ya fitar, bayan da gwamnatin jihar Legas ta dakatar da amfani da babura a wasu sassa na jihar.
Wannan matakin na gwamnatin Legas ya tilasta wa kamfanin nasa ya koma amfani da baburan domin jigilar kaya a madadin ɗaukan fasinja.