Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta hana daliban Saudiyya tashi a jirgin sama
Amurka ta dakatar da tashi a jiragen sama ko atisaye na daliban soji na Saudi Arabi a fadin sansanonin kasar, bayan mummunan harin bindika da wani sojin Saudiyyar ya kai ranar Juma'a a Florida.
Hukumomin Amurkar sun dakatar da duk wani atisaye na sama na daliban sojin amma, za a ci gaba da karantarwa a azuzuwa.
Muhammad Annur Muhammad na dauke da Karin bayani:
Wannan mataki na dakatar da duk wani atisaye na daliban sojin na Saudiyya a fadin Amurka, ya kasance ne bayan da Sakataren Tsaro na Amurkar Mark Esper, ya bayar da umarnin gudanar da nazari da sake tsari kan aikin koyarwar, sakamakon harin bindigar da wani sojin sama na Saudiyyar mai mukamin laftana ya kai a wani sansanin sojin ruwa na Amurkar a Florida, inda ya yi nasarar hallaka sojoji uku, da raunata wasu mutanen 8 ciki har da soji biyu.
Harin da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurkar, FBI ta ce tana kokarin gano sanadi ko dalilin da ya sa maharin, wanda 'yan sanda suka harbe, ya aikata shi, ko da yake dai masu binciken sun ce suna ganin ba zai rasa nasaba da ta'addanci ba.
Lamarin dai ya sa hukumomin Amurka cikin sake nazari kan dadaddiyar alakar da ke tsakanin Amurka da Saudiyyar.
Kawancen da daman tuni ya dan sukurkuce sakamakon hare-haren sojin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen da kuma kisan gillar mai sharhi a jaridar Washington Post, dan jarida Jamal Khashoggi, wanda ake zargin hukumomin kasar da hallakawa a shekarar da ta wuce.
Wata hafsa a sojin ruwan Amurka, Megan Isaac ta yi wa BBC Karin bayani game da umarnin dakatar da atisayen na daliban na Saudi Arabia, inda ta ce tun daga ranar Litinin ne aka fara aiwatar da shi.
Ta ce, dakatar da atisayen ya shafi daliban Saudiyya 303 a tashoshin jirgin sama na sojin ruwa uku da ke Florida, tashoshin Pensacola da Whiting Field da kuma Mayport.
Shi ma kakakin farar hula na hedikwatar tsaron Amurka, Pentagon, Chuck Prichard ya gaya wa BBC cewa dokar hana tashi a jirgin saman ta shafi dukkanin daliban Saudiya masu koyon tukin jirgin sama a fadin Amurka.
Ya ce matakin ya shafi daliban Saudiyya 852 Saudi da ke cikin duk wani shiri ko karatu na harkokin soji a Amurka, ko da yake za a ci gaba da ba su horo da karantarwa ta aji.
Sai dai wani babban jami'in ma'aikatar tsaron Amurkar ya sheda wa kafar yada labarai ta CBS cewa dakatarwar za ta tai ta akalla kwana biyar ne zuwa goma.
Hukumomin Amurkar sun ce ma'aikatar tsaron kasar tana sake gudanar da nazari kan tantance dukkanin daliban soji dubu biyar na kasashen waje da ke samun horo a Amurkar.
Haka kuma anumarci manyan jami'an tsaro na Amurkar da su sake duba tsarin matakan tsaro a sansanonin soji.
Shi ma dai Shugaban kasar Donald Trump ya yi alkawarin sake nazari kan duk wan shiri da ya jibanci sojojin waje.
Hukumar FBI ta Amurkar dai ta ce sojin Saudiyyar da ya kai harin na ranar Juma'a Mohammed Alshamrani mai shekara 21 ya sayi bindigar da ya yi amfani da ita ne wajen kai harin a Amurka, a ka'ida.