Iran ta zartar ta hukuncin kisa kan mai yi wa CIA ta Amurka leken asiri

A handout photo shows a missile being fired from a mobile launch vehicle during an Iranian military exercise in the Gulf of Oman (18 June 2020)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shirin nukiliyar Iran na daga cikin mafi karfi a Gabas Ta Tsakiya
An wallafa

Iran ta ce ta zartar da hukuncin kisa kan wani tsohon ma'aikacin ma'aikatar tsaro da aka same shi da laifin sayar wa Amurka bayanai.

A makon da ya gabata ne aka yanke wa Reza Asgari hukuncin, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar tsaro Gholamhossein Esmaili ya shaida wa 'yan jarida.

Mr Esmaili ya ce Asgari ya mika wa hukumar CIA ta Amurka bayanai kan shirin nukiliyar Iran bayan da ya bar aiki a sashen sararin samaniya na ma'aikatar tsaro a 2016.

Bai fadi yadda aka kama Asgari da gurfanar da shi a gaban kotu ko yadda aka yanke masa hukunci ba.

Mr Esmaili ya yi wannan sanarwa ce a yayin da yake amsa tambaya kan wani mutum wanda aka yanke masa hukunci kan leken asiri, Mahmoud Mousavi-Majd.

An yanke masa hukuncin kisa kan bayar da bayanan sirri ga CIA da hukumar leken asirin Isra'ila Mossad, wajen bibiyar dakarun Iran a Syria.

Amurka ba ta mayar da martani kan kisan Asgari ba.

A watan Yulin bara, ma'aikatar leken asirin Iran ta ce ta tsare mutum 17 da ake zargin su da karbar bayanai kan shirin nukiliyar kasar suna bai wa CIA. Ma'aikatar ta ce an yanke wa wasu hukuncin kisa amma ba ta bayyana sunayensu ba.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da sanarwar a matsayin "karya tsagwaronta".

A watan da ya gabata, an yanke wa wani tsohon dan kwangila na ma'aikatar tsaron Iran, Jalal Hajizavar, hukuncin kisa bayan samun sa da laifin leken asiri. Hajizavar ya amsa laifinsa da cewa an biya shi ne don ya yi wa CIA leken asiri.