Hotunan abubuwan da suka faru a Afrika a makon - 3 zuwa 9 ga watan Yuli 2020

An wallafa

Fitattun hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afrika da sauran sassa na wannan makon:

Wasu matasa na koyon rawa a Lagos a Nigeria, ranar Juma'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu matasa na koyon rawa a Lagos a Najeriya a ranar Juma'a.
Wata yarinya kenan ke rawar bude kafafu a aji.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Olamide Olawale na daya daga cikin dalibai 12 a Kwalejin koyon kida da rawa ta Leap Dance wanda David Ajala ke koyarwa kyauta.
Wasu masu zanga-zanga da ba a san ko su waye ba, sun taru wuri guda inda wani mutum daya ke rawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar kenan 'yan kabilar Oromiya daga Habasha da ke zaune a birnin St Paul na Amurka suna makokin mutuwar mashahurin mawakin nan Hachalu Hundessa wanda aka kashe a Addis Ababa a makon da ya gabata abin da ya haifar da fushi da tashin hankali.
Wata uwa kenan rike da 'yan tagwaye ta na murmushi. An nannade musu kai da bandeji bayan an yi musu tiyata.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Talata Ermine Nzotto daga Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya rike da 'yan tagwayenta Ervina da Prefina, wadanda aka haifesu a hade, bayan yi musu tiyata a kasar Italiya.
Mai wasan zamiya kenan yayin da igiyar ruwa ke kadawa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani dan Afrika Ta Kudu kenan James Bain ke wasan zamiya a Kogin Dungeons ranar Lahadi.
Daliban sakandare kenan a cikin aji.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu dalibai kenan a Afrika ta Kudu ciki har da daliban makarantar Sterkspruit a gabashin Cape Town lokacin da suka koma makaranta a wani bangare na fara bude makarantu ranar Litinin.
Mutane na kallon jaridu wadanda suka bayar da rahoton mutuwar Firaministan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mutane na juyayin mutuwar Firaministan Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly inda hotunansa suka cika jaridu.
Wani mutun sanye da kayan gargajiya bisa kan doki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Janar Khalifa Haftar na Libya, wanda yunkurin da ya yi na hambarar da gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ya ci tura, inda suke nuna rashin amincewarsu da taimakon da kasar Turkiya ke yi a Libya ranar Lahadi.
Wani mutum kenan ya ke tafiya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kasar Sudan na daya daga cikin kasashen Afrika da suke sassauta dokar kullen cutar korona. Wani ma'aikacin kiwon lafiya kenan a birnin Omdurman a ranar Laraba.
Wasu takalma kenan bisa teburi a birnin Abujar Najeriya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu takalma kenan bisa teburi a birnin Abujar Najeriya
Mutum-mutum Yesu almasihu kenan a yankin Turkana na kasar Kenya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mutum-mutumin Yesu Almasihu kenan a yankin Turkana na kasar Kenya.

Hakkin Mallakar Hotuna na AFP, Getty Images, EPA da kuma Reuters.