Coronavirus Bolsonaro: Kalaman kurin da Bolsanaro ya dinga yi kan korona kafin ya kamu da ita

An wallafa

Tun farkon barkewar annobar korona, shugaban Brazil Jair Bolsonaro ke raina girman barazanar da take haifarwa a duniya, duk da cewa cutar mai saurin yaduwa zuwa 6 ga watan Yuli ta kashe mutum a kalla dubu 65, sannan sama da miliyan 1.6 sun kamu da ita.

Bolsonaro ya sha kushe ka'idoji da sharuddan kare kai daga kamuwa da cutar da jami'an lafiya ke yawan gargadi a kai, sannan ya sha nuna adawa kan batun bai wa juna tazara.

A ranar Talatar (7 ga watan Yuli), shugaban mai tsattsauran ra'ayi ya gudanar da taron manema labarai inda ya tabbatar da cewa ya kamu da Covid-19.

Ga wasu kalaman shugaban masu tattare da ce-ce-ku-ce a kan annobar:

''Zuzutawa''

A daya daga cikin jawaban da ya yi wa al'ummah kan barkewar annobar, a ranar 9 ga watan Maris, lokacin da ya kai ziyara Amurka, shugaban ya ce kafofin yada labarai na zuzuta bazuwar Covid-19.

''Akwai batun da ake na coronavirus, wanda a ganina ana zuzuta girman barnar da cutar za ta iya,'' a cewar shugaban a wani taro da ya je a Miami.

'Yan kwanaki bayan wadannan kalamai, sama da jami'an gwamnatinsa 20 aka gano sun kamu da cutar, ciki har da wadanda suka masa rakiya zuwa Amurka.

'Yar mura'

Bayan mako biyu, lokacin da kasashe da dama a duniya ke cikin dokar kulle, shugaban ya soki matakan rufe makarantu da wuraren kasuwanci.

Bolsonaro ya kuma bayyana cutar a matsayin 'yar mura'' sannan ya ce ba ya fargabar kamuwa da ita.

''Ni da aka taba suka, 'yar mura ba za ta kassara ni ba,'' a cewar shugaban, inda yake nufin harin wuka da aka kai masa a zagaye na biyu na zaben shugabanci kasar da aka gudanar a 2018.

'Sauran mutane za su fi mu shan wahala.'

Bolsonaro ya yi ikirarin cewa annobar ba za ta yi wani tasiri sosai a Barzil ba, saboda ba su da mutane masu yawan shekaru sosai a kiyasi, idan aka kwatanta da wasu kasashen.

''Cutar za ta fi yiwa sauran mutane illa a kanmu. Tsoffin mutane da ke cikin al'ummar Turai sun fi namu yawa,'' a cewarsa.

A ranar 8 ga watan Yuli, Amurka ce kawai take da yawan mamatan da suka zarce Brazil sakamakon wannan annoba.

'Ku nemi hanyar shiga wuri ku dauki hoto'

A ranar 12 ga watan Yuni, Bolsonaro ya bukaci magoya bayansa su shiga asibitoci da kamarorinsu su duba yawan mutane da ke kwance a sashin samun kular gaggawa.

Shugaban a bainar jama'a ya kalubalanci rahotanin da ke cewa sashin lafiyar kasar ko asibitoci sun cunkushe saboda yawan mutane da ake kwantarwa sakamakon Covid-19.

"Ku nemi hanya ku shiga wurin ku dau hoto," a cewar Bolsonaro.

"Akwai bukatar a nuna musu ko ana amfani da gado ko a'a."

Mahukunta a fanin lafiya sun soki bukatar shugaban, wanda suka ce kokari ne na jefa rayuwa a cikin hadari.

"Kowa zai mutu wata rana"

A watan Maris, Bolsonaro ya tsaya tsayin-daka cewa wadanda jikinsu ke da rauni kawai za a killace.

An sha nuna shugaban a taruka daban-daban ba tare da ya mutunta umarnin bai wa juna tazara ba.

"Wannan zahiri ne, akwai wannan cuta. Dole mu fuskance ta, amma cikin hankalinmu. Ba wai kamar wasu yara ba," a cewar Bolsonaro a cikin yanayi na tinkaho.

"Rayuwa ce. Duk zamu mutu wata rana," In ji shugaban.

'Sai me?'

A karshen watan Afrilu, alkaluman mutanen da korona ta kashe a Brazil sun zarce na China.

'Yan jaridu su jefawa Bolsonaro tambaya kan wane tsokaci zai yi kan yawan karuwar mace-mace da ake samu sakamakon wannan cuta a kullum. Sai ya mayar da martani yana mana mai cewa:

"Sai me? Ku yi mun afuwan. Me kuke so na yi? Sunana Messiah, kuma bana siddabaru," a cewarsa, wato yana nufin sunan da yake amfani da shi a harshen Portugal kenan.

Sannan daga baya ya tambayi ko akwai mai nadar bayanansa - tare da nuna alhininsa kan mace-macen da ake yi.

"Na yi nadamar halin da muka shiga sakamakon wannan annoba. Muna mika ta'aziyar mu ga iyalan da suka rasa 'yan uwa da masoya, wanda akasari manya ne.

"Na aikata laifi - Ina ta hada liyafa"

Sama da mutum dubu tara suka mutu sakamakon annobar korona a Brazil, sannan akwai mutum dubu 135 da suka kamu da cutar lokacin da shugaba Bolsonari a ranar 7 ga watan Mayu ya sanar da cewa ya hada liyafar mutane 30 a gidansa da ke Brasilia.

"Na aikata laifi - Ina ta hada liyafa," kamar yadda ya ke shaida wa 'yan jarida.

Kwana biyu da wadanan kalamai, Bolsonaro ya yi amai ya lashe. Shugaban ya ce babu wata liyafa da ya hada zolaya yake yi.

'Babu abin da za a fasa a rayuwa'

A ranar da ya sanar da cewa gwaji ya tabbatar yana dauke da korona, Bolsonaro ya fada wa taron manema labarai cewa yana jin "gajiya, rashin dadin jikinsa da ciwon gabobi".

Sai dai hakan bai sanyaya wa shugaban gwiwa ba, ya bayyana cewa babban kalubalensa a yanzu shine "tsayawa da kafafuwansa".

"Amma ka da a tsorata, a cewarsa. "Babu abin da za a fasa a rayuwa."