Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cutar bubonic plague: Mece ce cutar bubonic plague da ta bulla a China?
Hukumomi a China sun dauki matakan kariya bayan da aka samu bullar wata sabuwar cuta ta bubonic plague a tare da wani mutum a wani birni da ke yankin Mongolia.
A cewar rahotannin kasar, mutumin da ya kamu da cutar dan garin Bayannur kuma makiyayi - an killace shi kuma yana samun sauki.
Jami'ai sun an kuma bincike kan mutum na biyu da ake zargi da kamuwa da cutar, a cewar kafar yada labarai ta China Global Times.
A baya can cutar bubonic plague na daya daga cikin cutukan da suka dinga firgita duniya, amma a yanzu ana iya magance ta cikin sauki.
An samu bullar cutar karon farko ne ranar Asabar a wani asibiti da ke Urad Middle Banner, a birnin Bayannur. Har yanzu ba a fayyace yadda aka yi mutumin ya kamu da cutar ba.
Mutum na biyu da ake zargi da kamuwa da cutar wani matashi ne dan shekara 15, wanda ya taba wani kurege da wani kare ya faruto, kamar yadda Global Times ta wallafa a tuwita.
An dauki wani matakin sanar da hukuma da ya haramta farauta da cin dabbobin da ka iya kasancewa suna dauke da kwayar cutar plague, har zuwa karshe shekarar nan kafin a cire shi.
Mece ce cutar bubonic plague?
Kwayoyin cutar bakteriya ne ke jawo cutar bubonic plague, wacce ta taba zama mummunar annoba a tarihin annoba da suka shafi dan adam a duniya - wato annobar Black Death - wacce ta kashe mutum miliyan 50 a fadin Afrika da Asiya da Turai a karni na 14.
Tun daga sannan an dan samu barkewar wasu annobar. Ta kashe kusan kashi biyar na al'ummar Landan a lokacin annobar Great Plague ta 1665, a yayin da fiye da mutum miliyan 12 suka mutu sun bayan barkewar cutar a karni na 19 a China da Indiya.
Amma a yanzu ana iya magance cutar da magungunan kashe kwayoyin bakteriya wato antibiotics.
Idan har ba a magance cutar wacce ke yaduwa daga dabbobi zuwa mutane ta hanyar kudaje - to ana iya samun kashi 30 cikin 60 na mace-mace.
Alamun cutar sun hada da zazzabi mai zafi da jin sanyi da tashin zuciya da rashin karfin jiki da fitowar kaluluwa a wuya ko hammata.
Me cutar ke haifarwa?
Mutum na soma rashin lafiya idan ya kamu da cutar bayan kwana biyu zuwa shida.
Wani bangare na jikin mutum na kumbura, girma na iya kaiwa na kwan zakara, sauran alamomin cutar sun hada da zazzabi da ciwon-kai da na kwanji da yawan kasala.
Cutar na kuma shafar hunhu, na haddasa tari, ciwon kirji da wahala wajen numfashi
Kwayoyin cutar na kuma gurbata jini da haddasa cutar da ake kira septicaemia ko sepsis, wanda ke lalata bargo da rashin aikin wasu sassan jiki daga nan kuma sai mutuwa.
Wa take kamawa?
Mutane na kamuwa da cutar daga:
- Cizo daga kwari ko sauron da ke dauke da cutar
- Taba dabar dake dauke da cutar kamar bera da gafiya
- Shakar numfashi ko yawun mai dauke da cutar ko daba
- Maguna ko karnuka da suka samu cutar daga kwari ko cin beraye
- Yanzu haka China ta haramta farauta ko cin namun daji
- Gawar mutumin daya mutu sakamakon wannan cuta na iya yadata idan an taba ta.
Cutar tana da magani?
Amfani da maganin kashe kwayoyin cuta na da muhimmanci. Cutar tana kisa cikin gaggawa.
Gano cutar kan lokaci, gwajin jini da sauran gwaje-gwaje, na iya ceto rayuka.
Ko akwai yiwuwar barkewar wata annobar?
Ba a faye samun bullar cutar bubonic ba, amma tana sake yaduwa daga lokaci zuwa lokaci.
An samu mutum 300 masu dauke da cutar a Madagascar yayin barkewar ta a 2017. Amma wani bincike na jaridar The Lancet ya gano cewa mutum 30 ne suka mutu.
A watan Mayun bara, mutum biyu sun mutu a Mongolia sakamakon plague, wadda suka kamu bayan da suka ci danyen naman kurege.
Sai dai babu tabbas kan ko sabbin masu kamuwa da cutar zai jawo annoba.
Dr Shanti Kappagoda wani kwararren likita ne nacutuka masu yaduwa a Stanford Health Care, ya ce: "Ba kamar a karni na 14 ba, a yanzu mun gane yadda cutar ke yaduwa.''
''Mun san yadda za mu dauki matakan kariya. Muna kuma iya warkar da masu dauke da ita da magungunan antibiotics.''