Hotunan Afirka na makon jiya: Mai aikin kashe gobara, masu haƙan kabari

An wallafa

Zaɓaɓɓun hotuna Afirka da 'yan Afirka a wata nahiyar na makon jiya.

Passengers wait on a bus called "Car Rapide" to be full at a bus station in Dakar, Senegal - 24 June 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fasinjoji suna cikin mota suna jiran ta tashi don tafiya inda za su je a Dakar, babban birnin Senegal ranar Laraba.
Sudanese revolutionaries paint murals along a wall in the Khartoum neighbourhood of Arkawit on 24 June 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar ce, a can Sudan masu fafutuka suka yi amfani da fenti wajen zana wasu hotuna don tunawa babban gangamin da aka yi a kasar a bara na bijirewa rundunar sojan kasar
A girl carries grilled corn cobs from the stall of a pedlar on the side of a main road in Libya's capital Tripoli - 24 June 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kazalika ranar Laraba, wannan yarinyar ta sayi gasasshiyar masara a Tripoli, babban birnin Libya.
A firefighter sprays water to extinguish a fire at the site of an accident after multiple fuel tankers spilled their cargo on a bridge along Lagos-Ibadan expressway in Lagos, Nigeria - 21 June 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani ma'aikacin kashe gobara a Najeriya yana aikinsa bayan tankokin man fetur niyu sun yi taho-mu-gama a kan titin Lagos-Ibadan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum daya ranar Lahadi
A suspended railway track at the site of a landslide that killed 13 people the day before, in Anyama, near Abidjan -19 June 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An samu tsaiko ga matafiyan da ke amfani da layin dogon da ya hada Abidjan, babban birnin Ivory Coast da Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, ranar Juma'a sakamakon zaftarewar kasa...
A suspended railway track at the site of a landslide that killed 13 people the day before, in Anyama, near Abidjan - 19 June 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Lamarin ya yi sandin mutuwa a kalla mutum 13 a kauyen Anyama da ke arewacin Abidjan...
An armchair among rubbles at the site of a landslide that killed 13 people the day before, in Anyama, near Abidjan - 19 June 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gidaje a kalla 20 sun lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka.
Tanzanian small-scale miner Saniniu Kuryan Laizer, 52, poses with the enlarged cheque copy from the government after selling two of the biggest of the country's precious gemstones, Tanzanite, during the ceremony for his historical discovery in Manyara, northern Tanzania - 24 June 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan mai aikin haƙar ma'adinan dan kasar Tanzania ya kuɗance cikin dare ɗaya bayan ya sayar da wasu duwatsun Tanzanite biyu - wadanda su ne irinsu mafi girma da aka taɓa haƙowa a ƙasar - a kan £2.4m ranar Laraba.
A Burundian refugee Bazira Afros, 26yrs old, who fled his country due to election violence, poses for a photo next to a footbridge where he and other refugees sleep next to a highway, ahead of World Refugee Day in Nairobi, Kenya, 19 June 2020.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani dan gudun hirar Burundi, Bazira Afros, mai shekara 26, ya tsaya dan dauki hotonsa a Kenya gabanin bikin Ranar 'Yan Gudun Hijira ta duniya wanda ake yi a ya Asabar.
Presentational white space
Protesters, including many motorbike-taxi drivers, hold placards while protesting and facing the police around parliament on for the second consecutive day in Kinshasa, DR Congo - 24 June 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Shugaba Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo suna zanga-zangar adawa da sauyin da ake shirin yi wa bangaren shari'ar kasar ranar Laraba.
Six Libyan experts search for human remains during the exhumation of mass graves in Tarhuna, south-east of Tripoli, Libya -23 June 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kwararru a Libya suna neman gawarwakin da aak watsar a wani babban kabari a Tarhuna da ke kudu maso gabashin Tripoli ranar Talata bayan dakarun da ke biyayya ga dan tawaye Janar General Khalifa Haftar sun janye daga yankin.
A delegate from Angola looks on during the vote of a watered down resolution condemning structural racism and police brutality in the wake of the death of George Floyd at the United Nations Human Rights Council in Geneva, Switzerland - 19 June 2020.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata wakilyar Angola tana kallo a yayin da ake jefa kuri'ar da ke yin tir da muguntar 'yan sanda da wariyar launin fata a zauren Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Geneva ranar Juma'a. An dauki matakin bayan kisan da 'yan sanda suka yi wa bakar fatar Amurka George Floyd.

Pictures from AFP, EPA and Reuters