Michael Jackson: Waƙoƙin da kuka fi so na mawaƙin

A ranar Alhamis 25 ga watan Yuni ne tauraron mawaƙi Michael Jackson ya cika shekara 11 da mutuwa bayan shekara kusan shekara 40 yana jan zarensa a fagen waƙa.
Mawaƙin ɗan Amurka ya karaɗe lungu da saƙo na duniya da waƙoƙinsa, waɗanda da ya fara tun bai balaga ba kuma da alama har duniya ta tashi ba za a manta da su ba.
Michael Jackson ya rasu ranar 25 ga watan Yunin 2009 yana da shekara 49 bayan ya sha wasu kwayoyi fiye da kima, a cewar rahotanni.
Daga cikin irin ra'ayoyin da kuka bayyana mana, mun tsakuro irin waƙoƙin da suka burge ku kuma kuke tuna shi da su.
Waƙar They Don't Care About Us ta yi fice matuƙa tun bayan sakinta a shekarar 1995 kuma samari a ƙasar Hausa musaman waɗnda ba su ƙware a Ingilishi ba kan ba ta sunaye iri-iri.
Wani mai bibiyarmu mai suna @bukarkundila a shafin Twitter ya ce shi waƙar da ta fi burge shi ita ce "awara da yaji da ɗumi-ɗuminta", yana nufin "They Don't Care About Us".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Yayin da @bendalhat ya ce shi waƙoƙin Thriller da Beat it ne ke tuna masa da Michael, shi kuwa @ybmmaskira Bellie Jean ya fi tunawa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

Karshen labarin da aka sa a X, 3
A shafinmu na Facebook kuwa, Mayor Muhammad Yusuf ya bayyana cewa ya taɓa ganin tauraron mawaƙin a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato UAE kuma waƙar Heal The World ya fi so.

Asalin hoton, Facebook
Babangida Nayilwa Bungudu ne ya ce duk da cewa shi ba ma'abocin waƙe-waƙe ba ne amma ya san cewa mawaƙin ya shahara.

Asalin hoton, Facebook
Shi ma Ahmad Ibn Aliyu Khamaaraway shi ya yi cewa waƙoƙi biyu ne suke burge shi - Thriller da Man in The Mirror- kamar yadda ake iya gani a ƙasa.

Asalin hoton, Facebook
Shafinmu na Instagram ma ba a bar shi a baya ba, inda mutum fiye da 250 suka bayyana ra'aytyoinsu game da shahararren mawaƙin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
@zeezee_sko ta ce waƙar Human Nature ce ta fi burge ta, sai kuma @aminu_keanuwess da ya ce waƙoƙin You Are Not Alone da kuma Billie Jean ne nasa.