Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Abuja: Ma'aikata sun yi zanga-zanga a Abuja
Ma'aikatan wucin-gadi da ke aikin yaki da cutar korona a babban birnin Najeriya Abuja, sun yi wata zanga-zanagr lumana saboda abin da suka ce rashin biyansu hakkokinsu da hukuma ta ce a ba su.
Ma'aikatan sun ce duk da irin sadaukar da rayuwarsu da suke yi suna aiki ba dare ba rana, hukumomin lafiya na babban birnin sun ki biyansu hakkokinsu ba kuma tare da wani bayani ba.
Ma'aikatan wadanda yawansu ya kai hamsin sun yi zanga-zanagr ta lumana ne a sashin kula da lafiya na babban birnin Najeriya Abuja ranar Litinin.
Da damansu sun ce sun dauki matakin ne bayan bin duk hanyoyin "lalama da magiya" ga shugabanninsu kan cewa a biya su hakkinsu.
A cewar wasu masu zanga-zanagar tuni wasu daga abokan aikinsu suka kamu da cutar, amma a cewar su hakan ba ta sa hukumomin sun duba halin da suke ciki ba.
Daya daga masu zanga-zangar ta shaida wa BBC cewa an biya ta Naira dubu 50 ne kawai a watan farko da ta fara aikin, amma tun daga nan a cewarta, ba a sake ba ta ko kwabo ba, duk da cewa ta kamu da cutar.
"Na samu ciwon nan a nan, na je wajen kula da masu cutar. Na warke sannan na dawo nan kuma na ci gaba da aiki amma ba a biya ni ba. Kuma ni ba zan ci gaba da aiki ba ina saka raywuta cikin hadari, kuma ba a biya na," in ji wata ma'aikaciyar da ba ta bayyanawa BBC sunanta ba.
Shi ma wani daga masu zanga-zangar mai suna Christopher wanda ya ce shi direban mota ne, ya ce tun da ya fara aikin tsawon wata uku ba a biya shi komai ba.
"Direbobi biyar ne suka kamu da cutar korona saboda da aikin, amma duk da haka ba wani abin da aka ba mu," a cewar Christopher.
Ya ce abin da yake ci musu tuwo a kwarya shi ne, duka abokan aikinmu da suke aiki a cibiyoyin killace mutane, duka an biya su kudinsu.
"Mu a nan ana barinmu ba wajen kwana ... muna ciyar da kanmu, muna biyan kudin mota mu zo nan ... dukkanmu nan muna da iyali," in ji Chirstopher, lokacin da yake magana da BBC cikin fushi.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ma'aikatan suka yi zanga-zanga kan neman biyansu hakkokinsu ba, ko a farkon watan nan Yuni sun yi irin wannan zanga-zangar.
Sai dai sashin kula da lafiya na babban birnin tarayya ya lasa musu zuma a baki a cewar su, inda ya ce za a shawo kan matsalar cikin kankanin lokaci.
A lokacin wata babbar jami'ar ofishin ta shaida wa BBC cewa za a shawo kan matsalar, alkawarin da suka ce ya zama gafara sa, amma ba su ga kaho ba.
Da BBC ta sake tuntubar jami'ar Dr Josephen Okechukwu bayan zanga-zanagar ta Litinin din nan, ta tana cikin taro, kuma ba ta da abinda za ta ce dangane da korafin m'aikatan.
To amma wani babban mai taimaka wa ministan Abuja na musamman Malam Ahmad Sajo ya ce hukumomin birnin tarayyar na Abuja sun amshi koken masu zanga-zangar, kuma za a biya su hakkokinsu ranar Laraba mai zuwa.