Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Facebook ya ce ya cire wani kamfe na Trump mai alamar 'yan Nazi
Facebook ya ce ya cire wani kamfe na Shugaba Trump na Amurka daga kafar sadarwar wanda ke dauke da wata jar alama da 'yan Nazi ke amfani wajen yi wa abokan hamayyarsu tambari kamar Freemasons da masu ra'ayin gurguzu.
An yi amfani da kamfe din da manufar kuntata wa 'yan Antifa wadanda Shugaba Trump da mukarrabansa ke yi wa kallon masu tsattsauran ra'ayi.
A 'yan makonnin da suka gabata lokacin da kamfanin Twitter ya cire irin wadannan sakonni na Donald Trump, Mark Zucherberg mai Facebook ya soki abin, inda ya ce ba ruwansa da yi wa 'yan siyasa shigege.
Facebook ya ce ya cire sakonni ne saboda suna dauke da kalaman kiyayya.
''Ba ma barin alamun da ke nuna ƙiyayyar wasu ƙungiyoyi ko wasu manufofi da ke nuna ƙiyayya sai dai idan an yi tur da su a cikin sakon,'' kamar yadda wani babban jami'i na kamfanin Nathaniel Gleicher, ya fada a ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa: ''Abin da ya faru kenan a wannan lamarin, kuma duk inda muka ga an yi amfani da wannan alamar to mataki iri daya za mu dauka.''
Tallar wadda aka sanya a shafukan Shugaba Trump da mataimakinsa Mike Pence ya shafe sa'a 24, kuma an gan shi sau dubun-dubata kafin a cire shi.
''Alamar da aka sanya din ta antifa ce, kuma tallar ta shafi antifa,'' kamar yadda mai magana da yawun ofishin kamfe na Trump Tim Murtaugh, ya fada a wata sanarwa.
"Kuma mun lura shima kamfanin Facebook yana amfani da irin wannan tambarin jan, wanda yake kama sosai da wanda muka yi amfani da shi,'' kamar yadda ya ce.
A bya-bayan nan Mista Trump ya soki antifa da fara wasu zanga-zanga a kan tituna a fadin Amurka kan mutuwar bakar fatar nan George Floyd.