Coronavirus: 'Ba za a sami riga-kafi a bana ba'

covid19
An wallafa

Kasashen Turai hudu sun kulla wata yarjejeniya da kamfanin hada magunguna na AstraZeneca domin samar da rigakafin cutar korona ga mutum miliyan dari hudu daga karshen shekarar nan.

Wannan ce yarjejniya irin ta ta farko da wata hadakar kasashe suka kulla da domin samar wa dukkan kasashen Tarayyar Turai isasshen rigakafin.

Tuni kamfanin AstraZenca ya fara gwaje-gwaje kan wani rigakafin da jami'ar Oxford ta kasar Ingila ta samar, amma babu tabbacin zai biya bukatun da ake bukata.

Kamfanin ya ce ba zai nemi cin riba daga aikin hada rigakafin ba.

checking for coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Peter Hotez, wanda kwarare ne a fannin ilimin rigakafi a Baylor College of Medicin da ke jihar Texas ta Amurka na cikin masu taimakawa wajen samar da wani rigakafin da kwalejin da yake aiki ke jagoranta tare da hadin gwuiwar wani asibitin yara na jihar ta Texas.

Ya ce samar da rigakafi aiki ne maii daukan tsawon lokaci matuka:

"Wadannan manya-manyan kokarin da ake yi na da muhimmanci. Saboda haka ina ganin wasu na kuskuren mayr da shi batun samun wani kamfanin da zai rika hada maganin ne - tamkar a ce muna da rigakafin a hannun mu ne."

Ya kuma ce: "Babban kalubale da ke gaban mu - ban da hada magani - shi ne nan da shekara daya ko biyu mai zuwa, a tabbatar cewa rigakafin na aiki kamar yadda aka tsara kuma baya cutar da masu amfani da shi."

Likita Hotez ya kuma ce babu yadda za a iya tattaro bayanan dubban wadanda ake gwajin rigakafin a jikinsu har a san ko ainihin yana aiki ko ba ya yi kafin nan da a kalla shekara daya mai zuwa.

Wannan na nufin karara cewa babu yadda za a iya samun rigakafin annobar korona cikin wannan shekarar da muke ciki, kuma tilas kasashen duniya sun samar da tsare-tsare da za su ci gab da kare al'umominsu har lokacin da aka samar da rigakafi mai inganci.