George Floyd: 'Al-Qaeda na ƙoƙarin ɓata tsakanin Amurka da masu zanga-zanga'

    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC security correspondent
  • An wallafa

Ƙungiyar al-Qaeda na ƙoƙarin amfani da rikicin da ke faruwa a Amurka domin cimma wata manufa inda suke neman Musulmai da waɗanda ba Musulmai ba su miƙa kansu a matsayin waɗanda aka zalunta.

Cikin abubuwan baya-bayan nan da aka wallafa a mujallar ƙungiyar mai suna "One Ummah," ta yi amfani da hoton George Floyd wanda ke nuna yadda 'yan sanda suka murƙushe shi - 'yan kungiyar na goyon bayan masu zanga-zangar.

Saƙon dai wanda aka rubuta da Turanci an yi shi ne domin 'yan Amurka, inda ake hasashen rushewar tsarin siyasar Amurka da kuma tattalin arzikinta.

"Zanga-zangar da ake yi ɗauke da makamai ta mamaye kusan ko ina a cikin Amurka kuma yaƙin basasa da alama yana gab da afkuwa," irin saƙon da suka fitar kenan inda kuma suka ce "ko 'yan jam'iyyar Democrats ba za su iya taimakonku ba amma mu za mu iya".

Mina Al-Lami, wadda ke ɓangaren bincike na BBC Monitoring, ta bayyana cewa akwai bambanci tsakanin ƙungiyar al-Qaeda da kuma abokiyar adawarta wato Islamic State (IS).

Kungiyar IS na ta nuna jin daɗinta kan yadda ake rikici a Amurka inda suke cewa rikicin zai bazu zuwa wasu ƙasashe, sai dai kuma al-Qaeda na bi a hankali inda suke neman wasu 'yan Amurka da su bi irin aƙidarsu.

Wani mai yi wa BBC fashin baƙi kan al'amuran yau da kullum ya bayyana cewa wani wanda ya san sirrin abin da ke faruwa a Amurka ya rubuta wannan mujallar.

Neman dawowa

A cikin 'yan shekarun nan, kungiyar IS ta shafe ayyukan al-Qaeda inda ta fi ta tasiri. Amma Dakta Shiraz Maher, wanda shi ne darakta na cibiyar karatu kan masu tsattsauran ra'ayi a Landan na ganin cewa ƙungiyar al-Qaeda na koƙarin nuna cewa har yanzu tana da muhimmanci a duniya.

"Batun zanga-zangar ''rayuwar ɓakaƙen fata na da muhimmanci'' babban abu ne da ya zagaye duniya... zanga-zangar na tasiri a faɗin duniya," in ji Dakta Maher.

"Al-Qaeda na ƙoƙarin kutsawa cikin wannan lamari inda suke so su nuna cewa su ma suna nan daram."

Ana ganin kamar wani wasan kwaikwayo ne sakamakon ɗaya daga cikin ƙungiyar da ta shahara wajen kisa da kuma zalunci a Gabas Ta Tsakiya na miƙa kanta ga 'yan Amurka a matsayin ɗaya daga cikin mai goyon bayansu kan irin zaluncinda 'yan sanda ke yi musu a ƙasar.

Kungiyar al-Qaeda ƙarƙashin jagorancin Osama Bin Laden ta ƙaddamar da harin ta'addanci mafi muni a 2001 a tarihin Amurka, ƙungiyar ta taɓa saka wata doka a lardin Falluja na Iraƙi inda ake yanke wa mutane yatsu idan aka kama su shuna shan sigari.

Hakan ya kawo rikici matuƙa a faɗin duniya.

An shafe watanni shugabannin hukumomin da ke tattara bayanan sirri na ƙasashen yamma na ta gargaɗin cewa al-Qaeda na nan bata rushe ba, tana nan tana jiran wata dama.

A wannan shekarar, ƙungiyar al-Qaeda da kuma ta IS na ta murnar yadda annobar Covid-19 ta yi mummunar shafar Amurka da Burtaniya, suna masu cewa alhakin abin da kasashen biyu ke yi a Gabas Tsakiya ne. Yayin da Iran ke da mutum 175,000 masu cutar, sannan Masar ma na ci gaba da samun karuwar masu cutar.