Sojojin Kamaru: An tuhumi uku daga cikin su da laifin kisa

An wallafa

An tuhumi sojojin Kamaru uku bisa laifin kisan kai a yankin Arewa maso Yammacin kasar a watan Fabrairu, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.

Da farko hukumomin kasar sun musanta hannun soji a kisan farar hula 13, cikinsu har da yara 10 a garin Ntumbo, amma a watan Afrilu fadar shugaban kasar ta amince cewa sojoji uku da 'yan bijilante sun kai samame a yankin 'yan a-waren kasar.

Ta ce ba da gangan aka yi kisan ba ko da yake sojoji sun yi yunkurin yin rufa-rufa kan kisan.

Gwamnatin Kamaru ta kwashe sekara uku tana kai ruwa rana da masu fafutukar ballewa daga kasar da ke yankin masu magana da turancin Ingilishi.

AFP ya ambato mai magana da yawun rundunar sojin kasar Kanar Cyrille Atonfack Guemo yana cewa: "An daure sojojin Kamaru uku a gidan yarin sojoji da ke Yaounde."