Lagos: An yi zanga-zanga kan kisan da 'yan sanda suka yi wa matashiya

An wallafa

A ranar Alhamis ne wasu matasa a birnin Legas suka gudanar da zanga-zangar lumana.

Zanga-zangar dai ta zo a lokacin da suke neman a hukunta wasu 'yan sanda biyu da kashe Tina Ezekwe 'yar shekara goma sha shida a bainar jama'a da gangan.

Masu zanga-zangar sun yi ta ihun ''Wanda ya kashe Tina ba zai yi mutuwar alheri ba.''

Sun karade tituna suna cewa an kashe Tina a a gaban jama'a. Saboda haka suke neman a bi kadin Tina da wani dan sanda ya bindige har lahira.

Masu zanga zangar sun rike kwalaye da aka rubuta cewa ''ku daina kashe mu, ku kare lafiyarmu.''

Jagoran zanga-zangar Kunmle Ajayi, ya wuce gaba yana magana a yayin da sauran masu zanga-zangar ke maimaita abin da yake fada.

Ya ce: ''Muna wannan waje kamar yadda kake gani inda anan ne aka kashe Tina. Sun kashe mutane da yawa rike da bindiga kuma suna jin dadin kashe mutane.

''Muna neman a bi hakkin Tina da sauransu. Akwai da yawa da suka fada cikin taskun 'yan sanda. Akwai mutanen da suka shaida yadda aka kashe Tina.

''Tina dai an kashe ta. Muna son a hukunta 'yan sanda biyu da ake zargi da kisanta. Muna neman a biya diyyar naira miliyan 16. Muna neman duk wasu da aka yi wa fyade da kuma wadanda suka fada hannun 'yan sanda,'' a cewar jagoran.

Ya kara da cewa: ''Muna cewa a kawo karshen yadda 'yan sanda suke azabtar da mutane.''

Shi kuwa Samuel gabriel cewa ya yi: ''Mutanen Naijeriya ba dabbobi ba ne, bai kamata a dinga amfani da makamai sakaka a kanmu ba. Kar a sake amfani da nunawa farar hula bindiga a kansu.

''In ka taba budurwa ko ka taba dan Naheriya to muna cewa ba mu yarda ba.

Yana cewa in har jami'an tsaro suka taba wani farar hula to kamata ya yi mu fito mu kare kanmu.''

A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan sanda suka harbe wata yarinya da ake kira Tina, to amma wasu daga cikin jami'an suka yi ikirarin cewa harsashi ne ya kubuce kuma ya same ta bisa kuskure amma ba ita aka shiryawa muguwar kaddarar ba.

Tuni dai rundunar 'yan sanda ta kama dan sandan da ya aikata danyen hukuncin da kuma cewa za a gudanar da bincike domin daukar duk matakin da ya dace.

Rundunar 'yan sandan jihar Legas a ranar Litinin ta ce an fara gudanar da bincike kuma ana tuhumar 'yan sandan biyu da ake zargi da kashe yarinyar mai suna Tina Ezekwe, ya kuma nuna cewa 'yan sandan sun gaza kiyaye iyakokin da aka gindaya mu su a hukumance.

Tun a ranar Litinin ma'abota shafukan sadarwa suka fantsama don neman adalci ga Tina, wadda wani dan sanda mai farin jini ya kashe a yankin Iyana Oworo na jihar ranar Talata.

A yanzu dai 'yan sandan biyu za su fuskanci shari'a da a kan yi wa jami'ansu a cikin gida. Bayan nan ne za a gurfanar da su a gaban shari'a domin hukunta su.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu, ya ba da umarnin a gudanar da bincike mai zurfi game da yanayin da ke tattare da mutuwar Tina.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake zargin jami'an tsaro na 'yan sanda da harbe farar hula bisa karamin kuskure ko kuma fusata da in an yi hakuri ana iya kai zuciya nesa ba.