Trump na ƙoƙarin raba kawunan Amurkawa - Tsohon Sakataren Tsaro

Image shows U.S. President Donald Trump and former Defence Secretary James Mattis

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, James Mattis ne Sakataren Tsaron na gwamnatin Trump na farko - amma ya yi murabus a shekarar 2018
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon Sakataren Tsaron Shugaba Donald Trump, James Mattis, ya soki shugaban ƙasar da cewa yana jawo rarrabuwar kawunan mutane da gangan.

Ya ce ya ji taƙaici da al'ajabin ganin yadda Mista Trump ke yi wa lamarin zanga-zangar da ake yi kan kisan da 'yan sanda suka yi wa George Floyd riƙon sakainar kashi.

Mr Mattis ya yi Allah-wadai da ''take doka'' da Trump ke yi - ya kuma goyi bayan masu zanga-zangar da ke neman ɗaukaka darajar Amurka, kamar yadda tsohon shugaban kasar Barack Obama ya yi.

Mr Trump ya bayyana Mr Mattis a matsayin ''janar din da ke zuzuta abu.''

A shekarar 2018 ne Mr Mattis ya yi murabus bayan da Shugaba Trump ya yanke shawarar janye dakarun Amurka daga Syria.

Tun daga lokacin ya kame bakinsa, har sai a ranar Laraba da mujallar The Atlantic ta wallafa yadda ya ragargaji gwamnatin Trump.

A martanin da ya mayar kan sukar ta baya-bayan nan, Mista Trump ya wallafa jerin saƙonni a tuwita inda ya yi iƙirarin shi ya kori Mista Mattis.

''Ba na son tsarin shugabancinsa, da kuma abubuwa da yawa a kansa kuma wasu da dama ma sun yarda da haka,'' kamar yadda ya rubuta. ''Na ji ɗaɗi da ya tafi.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Wannan sa'insa dai na zuwa ne bayan da aka gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan dukkan jami'an 'yan sanda da aka kora daga aiki waɗanda a gabansu aka kashe Mista Floyd a birnin Minneapolis.

Ana tuhumar Derek Chauvin da mataki na biyu na kisan kai, yayin da sauran jami'an da a baya ba a tuhume su ba, yanzu suke fuskantar tuhumar taimakawa wajen kisan kai.

Mutuwar tasa ta jawo jerin zanga-zanga a faɗin Amurka cikin kwanakin nan.

Me Mattis ya ce?

"Donald Trump ne shugaban ƙasa na farko a tsawon rayuwata da ba ya ƙoƙarin haɗa kan Amurkawa - kuma ba ya ko ƙoƙarin gwadawa.'' Mista Mattis ya rubuta a mujallar The Atlantic. ''A maimakon haka sai yake ƙoƙarin raba kawunanmu.''

Ya ci gaba da cewa: ''Muna kallon yadda sakamakon abubuwan da aka shafe shekara uku ana yi da gangan ke kasancewa. Muna kallon sakamakon abin da yake faruwa a shekara uku na rashin shugabanci nagari.''

Mr Mattis ya kuma yi magana kan zanga-zangar da ake ta yi ta nuna wariyar lauyin fata.

Presentational grey line