Coronavirus a Kano: "Ban ji daɗi da zargin cewa ni na kawo cutar ba"

An wallafa

Mutumin da aka yi zargin cewa shi ne na farko da ya kamu da cutar korona a Kano, ya ce bai ji daɗin yadda aka yi ta yayata cewa shi ne ya kai cutar jihar ba.

Ambasada Kabiru Rabi'u wanda yanzu ya warke har ma an sallame shi daga asibiti, ya sha kakkausar suka da miyagun kalamai har da tsinuwa bisa zargin cewa ya kai korona jihar Kano da gangan.

Ranar Asabar 11 ga watan Afrilu ne, hukumomi suka sanar da ɓullar annobar a jihar, wadda a yanzu ta fi kowacce jiha yawan masu cutar a arewacin Najeriya.

Ya ce: "Cutar korona ba ganinta ake ba, bare ka ce ka gan ta, ka je ka ɗauko. Shi kuma wanda yake da ita, ba wata kama (ta daban) yake da ita ba, saboda haka bari ka je ka ɗauka a wurinsa ".

"Cutar da ba a ganinta da ƙwayar ido, ai abu ne mai wahalar gaske, mutum ya ce ya san inda ya ɗauke ta a wani lokaci kuma," in ji shi.

Ambasada Kabiru Rabi'u ya ce ya je Legas ranar 11 ga watan Maris kuma iyakarsa daga otel sai ofishin da ya yi ganawar da ta kai shi. "Ba zan ce na yi hulɗa da wani ko na ɗauko ta a Legas ba".

"Domin duk wa'yanda muka yi board meeting da su, babu wanda ya ce ya yi rashin lafiya. To, in dai a nan ne dole a samu wani da ke da cutar," in ji shi.

Ya ce bayan ya yi kwana biyu a Legas sai ya koma Abuja ranar 13 ga watan Maris har zuwa 25 ga wata, ni na so na zauna ma fiye da haka.... "amma sai aka ce za a rufe gari ba shiga ba fita".

A cewarsa: "Da na zo Kano sai da na yi wajen sati guda, ban ji ciwon kai ba, ban ji zazzaɓi ba, ban ji komai ba. Ina nan lafiya yau".

Ya ce sai daga baya ne ya fara jin zazzaɓi da tari, abin da ya sa shi zuwa ya siyo magani, kuma aka yi masa allurar maleriya. "Aka yi, aka yi amma ban ji komai ba".

Ambasada Kabiru ya ce a lokacin ne ya yi tunanin neman jami'an lafiya don su ɗauki samfurinsa su gani ta yadda zai san matsayinsa game da annobar da ke yaɗuwa a sassan Najeriya.

"So, ba zuwa suka yi suka ɗauke ni ba, kamar yadda wani likita ya faɗa cewa sun zo sun ɗauke ni a asibitinsa."

Ya ce shi ma bai san yana da cutar korona ba a lokacin. "Yaya zan gaya mai ina da cuta, bayan ni ma ban sani ba. Ko Allammusuru ne ni?"

Tsohon jakadan ya ce ya je asibitin likitan ne saboda ciwon ƙafar da ya yi fama da shi.

Kuma a lokacin ne ya ne, likitan ya faɗa masa cewa ya lura akwai ƙarancin ruwa a jikinsa, in ji Ambasada Kabiru. Ya kuma ce likitan ya sake tambayarsa abubuwan da yake ji lokacin a jikinsa.

"Na ce ina jin zazzaɓi lokaci-lokaci, amma dai bai kwantar da ni ba. Sannan ina jin tari da kaushin maƙogwaro.... To, ka ga ai shi ne yake da ilmin likita. Shi zai san waɗanne irin cutuka ne ke janyo irin waɗannan alamomi," a cewarsa.

Da aka tambaye shi game da zargin da wasu suka yi cewa ko kwangila aka ba shi ya kai cutar korona Kano, Ambasada Kabiru ya yi dariya. "Wannan ai magana ce ma da bai kamata...a ma yi ta ba".

"Ni yanzu wanne kuɗi ne ban riƙe ba a Najeriya? Wanne irin arziƙi ne da ake da shi a duniyar nan, Allah bai min ba? Allah Yai min arziƙin 'ya'ya, Allah Yai min arziƙin iyaye na-ƙwarai.

Ya yi min arziƙin karatu daidai gwargwado na arabiyya da na boko. Kuma ina da 'yan canji a aljihuna," in ji Ambasada.

Ya ce kuma duk da wannan baiwa "sannan na baro gidan da nake ni kaɗai, in taho inda iyalina suke zaun? Ai ka ga ban musu adalci ba.

(Kuma) in zan cutar da mutane, sai in tafi gidanmu? Inda iyayena suke? Ya tambaya.

Sannan kuma in je unguwarmu, in ɗauko abokaina da suke unguwar, su zo su zauna duk in sa musu cuta? Wanne irin hauka ne wannan?"

Ambasadan ya ce duk da yake ya mayar da lamarinsa ga Allah. Kuma ya ɗauki abin da ya faru a matsayin ƙaddara, amma bai yafe ba.

"Ban yafe musu ba! Dalili kuwa shi ne idan wani ya buga a shafukan sada zumunta, wani ya bayyana ra'ayinsa, to wannan zan iya yafewa. Amma wanda ya zauna ya ƙirƙiri labaran bogi a kan abin nan, shi ne ban yafewa ba, cewar Ambasada Kabiru.

'Har yanzu ina shan tsangwama'

Ya ce har yanzu da ya warke yana fuskantar tsangwama. "Mutane ko wucewa suka zo yi ta nan, sai sun nuna gidana, suna cewa ga gidan korona.

Abin mamaki sai ga shi har gwamna na Kano a cikin jawabansa ya zo yana cewa wai na zo Kaduna, na je na gaggaisa da abokai da sauransu (sannan) na taho Kano. Ambasada Kabiru ya ce wannan ba gaskiya ba ne.

Ya ce lokacin zamansa a cibiyar killace masu cutar korona tsawon kwana 29, ya fara karanta kalaman mutane a cikin waya, da tsinuwa da sauransu, amma sai ya daina.

Ambasada ya ce ya daina karanta kalaman mutane ne saboda ya ga abubuwan sun yi yawa, hatta rediyo sai da ya daina sauraro saboda kada hankalinsa ya ci gaba da tashi.

"Da ma ina cikin wani tashin hankali, to kada na ƙara wa kaina azaba, sannan in dinga karanta abubuwa suna daɗa ɓata min rai. Sai na ga ya kamata na daina karantawa," in ji shi.