Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Soja ya kashe mutum saboda wayarsa ta yi ƙara a Habasha
Wani soja a ƙasar Habasha ya harbe wani mutum bayan wayarsa ta yi ƙara yayin wani taron ganawa, a cewar ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International.
An harbe Ariti Shununde mai shekara 32 yayin wani samame domin kakkaɓe 'yan bindiga na Oromo Liberation Army (OLA), a cewar shaidun da Amnesty ta ambato.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mahukunta game da rahoton kisan amma ba su ce komai ba.
Sojojin sun kira wani taro na jama'ar gari a Oromia sannan suka karɓe wayoyin mahalarta taron.
Sai ɗaya daga cikin wayoyin ta yi ƙara. Sojoji suka tambayi wayar wace ce kuma nan take Ariti ya fito, kamar yadda wanda ya shaida lamarin ya bayyana.
Kawai sai aka harbe shi har sau biyu a baya, in ji mutumin. Amnesty ta ce wasu majiyoyin ma daban sun ruwaito labarin.
Wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da Amnesty ta ruwaito daga cikin irin ayyukan da sojoji ke yi na dakile 'yan tawayen yankin Oromia a ƙarshen shekarar 2018 zuwa 2019.
Ita ce shekarar da Shugaban Ƙasar, Abiy Ahmed ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.