Coronavirus: Me ya sa cutar korona ta mayar da ɓeraye mugaye?

An wallafa

Annobar korona ta sa an rufe gidajen cin abinci sannan ta tilasta wa mutane zaman gida.

Hakan ya jawo abbubuwa guda biyu; wajibi ne ɓeraye su nemi abincinsu a wani wuri daban sannan kuma su sauya ɗabi'unsu.

Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cutuka ta Amurka (CDC) ta yi gargaɗi a makon da ya gabata cewa, ɓeraye mayunwata za su iya "sabuwar ɗabi'a kuma mai cutarwa".

Gargaɗin ya nuna cewa rufe gidajen cin abinci "ya jawo ƙarancin abinci ga ɓeraye, musamman a wuraren da ke da yawan al'umma".

Ɓerayen na neman sabbin hanyoyin samun abinci, abin da ya ƙara yawan zirga-zirgarsu a faɗin duniya.

Babban misali shi ne taron casu da aka haɗa a watan Fabrairu a birnin Louisiana na ƙasar Amurka, inda dubban mutane suka taru a gidajen cin abinci da wuraren kaɗe-kaɗe, amma sai annobar korona ta tilasta musu rufe ƙofofinsu.

Su kuwa ɓeraye sai suka fito daga gidajen ɓuyansu kamar a sauran sassan Amurka - kamar a Washington da New York.

"Ma'aikatan tsafta da masu kula da ɓeraye za su fuskanci hauhawar neman buƙata da kuma rahotannin sabbin halayen ɓeraye," a cewar CDC.

Wani ƙwararre kan halayen ɓera mai suna Robert Corrigan a Amurka, ya ce wannan sabuwar ɗabi'a ba wai a kan mutane za su nuna ta ba, a kan sauran ɓeraye za ta ƙare da kuma wurare yayin da suke neman rami domin shiga da zummar samun abinci.

Ya ce: "Hakan ba ya nufin ba za su kai wa mutane hari ba."

Cin naman 'yan uwansu

Aƙalla kashi ɗaya bisa uku na al'ummar duniya sun sauya halayensu a 'yan watannin nan saboda wannan annoba.

A ƙasashe da dama, an taƙaita zubar da shara wadda kuma ita ce ɓeraye suka dogara a kai domin samun kai wa baka, kuma hakan ya sa ɓerayen suka saba.

A watan Afrilu, hukumar kula da ƙwari ta National Pest Technicians Association a Birtaniya ta yi gargaɗin cewa "rufe wuraren taruwar jama'a da na cin abinci da otel-otel zai jawo matsaloli".

Hukumar ta ce dabbobi masu ɓarna za su iya hayayyafa a wuraren da babu jama'a ko kuma su fita neman abinci, yayin da suke samun ƙwarin gwiwa daga yunwar da ke damunsu.

"Ɓeran da ke jin yunwa zai iya zama mai haɗarin gaske ga sauran ɓeraye," in ji Corrigan, wanda ya yi aiki a matsayin ƙwararre kan halayen ɓera ga kamfanoni da kuma gwamnatin Amurka.

Corrigan ya ce an samu hujja game da yadda ɓerayen suka riƙa kai wa juna hari da cin naman juna a wuraren da suka saba samun abinci, wanda a yanzu suka rasa.

Ya ƙara da cewa wannan ba sabon abu ba ne musamman a alokuta irin waɗannan.

'Ƙwararru wurin sabo'

Mayunwatan ɓeraye "ka iya yin nisan kiwo zuwa wata unguwa da babu ɓerayen a da," Corrigan ya faɗa wa BBC.

Masanin ya ce ɓeraye dabbobi ne masu basira wurin gano inda abinci yake sannan kuma haƙwaransu kan yi ɓula a jikin ƙofofi da robobi da ma raga.

"Suna nan a ko'ina kuma ba zai yiwu su karaɗe duniya ba idan har ba su da ƙwarewa wurin sabawa da yanayi," in ji shi.

Sai dai ƙaruwar yawan ɓerayen ba ya nufin za su fi mutane yawa.

Hasali ma, Corrigan ya ce yanzu ne ya kamata a fito da sabbin hanyoyin kariya.

Me ya sa ake ƙyamatar ɓeraye?

Tawagar ɓeraye mayunwata kan haddasa fitina, su lalata gida sannan su yaɗa cuta.

"Za su iya kasancewa a wani ɗaki mai cike da yara ko gidan gajiyayyu ko kuma asibiti," a cewar Corrigan.

Ana alaƙanta ɓeraye da cutuka kusan 55, duk da yake babu wani rahoto da ke alaƙanta su da cutar korona.

Yadda za a kori ɓeraye daga gida

Ɗaya daga cikin hanyoyin kare kai daga ɓeraye ita ce toshe ramuka da ke kusa da ƙasa. Haka abin yake ga sauran wurare kamar fayif da ɓera zai iya samun damar shiga.

A cikin gida, ku tabbata babu inda za su iya ɓuya, ta hanyar tsaftace ko'ina da ɗebe tarkace.

Yana da kyau a ɓoye kayan abinci a cikin abin da ɓera ba zai iya hudawa ba.