Coronavirus a Najeriya: Mutum 249 suka mutu, masu warkewa sun karu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Sabbin alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fitar a daren Talata sun nuna cewa wadanda suka kamu da cutar korona sun haura dubu takwas a Najeriya.

Alkaluman da ta fitar sun nuna cewa mutum 276 sun sake kamuwa, hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar 8,344..

Haka kuma hukumar ta ce wadanda suka mutu sun kai 249 a fadin kasar.

Har yanzu dai Jihar Legas ke kan gaba an samu karin mutum 161 da suka harbu, sai Rivers da ke mataki na biyu da mutum 36.

Jihar Edo na da mutum 27 sabbin kamu, sai Kaduna da alkaluma suka nuna an sake samun mutum 19 dauke da cutar.

Akwai jihar Nasarawa mai mutum 10, Oyo 6, Kano 4, sai Delta 3.

Sauran jihohin da suka fito a jadawalin sun hada da Ebonyi mai mutum 3, Gombe 2, Ogun kuma mutum 1.

Masu cutar korona a Ondo sun karu da mutum 1, Borno 1, kana akwai Abia da Bauchi inda aka samu mutum dai-daya.

Sai dai, daidai lokacin da ake ƙara samun adadin mutanen da cutar ke ƙara harba, haka kuma mutanen da suke warkewa su ma suna ƙaruwa. Yanzu dai mutum 2,385 ne aka tabbatar sun warke a Najeriya.

Kusan rabin mutanen da suka sake kamuwa da koronan suna Lagos, jihar da ta fi fama da annobar a Najeriya. Yanzu dai tana da masu cutar 3,756.

Jihar Kano ita ce ta biyu da yawan masu korona 923, sai Abuja na Uku da yawan masu korona 519.

Har yanzu a hukumance cutar korona ba ta ɓulla cikin jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na cewa mai yiwuwa akwai annobar cikinsu, kawai dai don ba a yin gwaji ne.

Muhimman bayanai kan annobar korona

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.

Har yanzu a hukumance ba a samu bullar cutar a jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na da ra'ayin cewa hakan ta faru ne saboda ba a gwajin cutar a cikin johohin biyu.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya adadin gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.

Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Talata 26 ga watan Mayu.