Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Najeriya: Yadda cutar 'ta kassara tattalin arzikin masu sayar da kaji'
A karon farko cikin gomman shekaru, za a gudanar da bikin Ƙaramar Sallah lami cikin jihohin Najeriya, don kuwa hatta hawan idi ma ba lallai ne a yi ba cikin wasu sassan ƙasar har da babban birnin Abuja.
Annobar korona wadda ta fantsama duniya tun farkon wannan shekara ta janyo ƙaƙaba matakan hana tarukan jama'a da na addini lamarin da kuma ya shafi bikin Ƙaramar Sallah a bana.
Matakan kulle da hukumomi suka ɗauka tsawon makwanni sun janyo taɓarɓarewar harkokin kasuwanci da na tattalin arziƙi. Magidanta da dama na cewa ko ɗinkin sallah ba za su iya yi wa 'ya'yansu ba.
Yayin da 'yan kasuwa kamar Anas Sa'idu mai sayar da kaji a unguwar Gwarinpa ya ce: "Gaskiya, sallar bara ta fi ta bana, saboda bara mun yanka kaza goma, ashirin, hamsin kai har sittin lokaci ɗaya a nan".
Amma bana sai dai kaza ɗaya, biyu, an saya da yawa guda goma, in ji shi.
A cewarsa: "Matsalolin da ake ciki har da na koronabairus, sun sa halin da muke ciki, kasuwa bana sai dai a hankali".
Wakilin BBC Ishaq Khalid da ya zanta da mai sayar da kajin ya ce mutane kaɗan ne ke zuwa sayen hajar da Anas Sa'idu ya kasa, sa'o'i kafin bikin Karamar Sallah.
Ishaq ya ce kamar yadda azumin bana ya kasance, haka ita ma Ƙaramar Sallah ta zo ga Musulmi a wani yanayi.
Galibin jama'a ba su taɓa ganin irin wannan al'amari ba a rayuwarsu, annobar korona ta janyo taƙaita zirga-zirga da hana taruka. Kuma a haka Musulmi ke tunkarar Ƙaramar Sallah, in ji Ishaq.
Malam Musa Mesil wani magidanci a Abuja ya faɗa wa Ishaq cewa yanzu dai ya zubawa sarautar Allah ido kawai.
Domin ba shi da kuɗin abinci, babu na kayan sallah, ga shi kuma hukumomi a birnin sun hana zuwa masallacin idi, don taƙaita yaɗuwar cutar, in ji Ishaq.
Musa Mesil ya ce batun kayan sallah da ni da yara, babu. "Domin ba ni da abin da zan sayar in yi musu".
Ya ce ga shi ma sallar ta riga ta zo. Kawai dai mun bar wa Allah al'amarinsa. Idan Ya kawo daga nan zuwa sallar.... ba mu sani ba.
Magidancin ya ce sai dai: "Mu ce inna lillahi wa inna ilaihir raji'un! Domin gabanin wannan lokaci, abubuwa duk sun zo sun tsaya gaba ɗaya."
A cewarsa tun lokacin da aka ce wannan cuta ta korona ta shigo Najeriya, kusan duk wani mai ƙaramin ƙarfi a ƙasar nan, yana cikin ha'ula'i. "Saboda duk abubuwan da muke yi ba sa tafiya".
Ishaq Khalid ya ce a galibin jihohin arewacin Najeriya ciki har da Kano, hukumomi sun janye dokar hana tarukan ibada..... Matakin da ya ba da damar yin sallar Juma'a da kuma Idi.
Yayin da a wurare irinsu Filato da Kaduna har ma da babban birnin ƙasar Abuja, ga dukkan alamu ba za a gudanar da tarukan sallar idi ba, don kuwa ba a sassauta dokar hana tarukan ibada ba.