Coronavirus ta kama mutum 6,401 a Najeriya, 1,734 sun warke

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Sabbin alkaluma da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta fitar a daren Talata sun nuna cewa masu dauke da korona yanzu haka a kasar sun kai 6,401.

Wannan ya biyo bayan samun karin mutum 226 da suka sake kamuwa da cutar a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Yanzu dai adadin mutane da cutar ta hallaka a fadin kasar ya kai 192, yayin da mutum 1,734 suka warke.

A Legas, jihar da ta fi yawan masu fama da korona, sabbin alkaluma sun nuna an sake samun mutum 131 da suka kamu.

Jihar Ogun ita ce ta biyu a jadawalin daren Talata da mutum 25 sabbin kamu.

Sai Plateau mai 15, Edo 13, Kaduna 7, Oyo 6, Jigawa da Ebonyi da kuma Borno masu mutum 4, 4.

Bauchi da Gombe kuma sun samu mutum 2, 2 sabbin kamu.

Birnin Tarayyar Najeriyar Abuja kuwa mutum 5 ne suka sake kamuwa da cutar.

Adamawa 5, da Nasarawa suna da mutum 3, sai kuma Enugu da Bayelsa mutum 1, 1 sabbin kamu.

Muhimman bayanai kan annobar korona

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.

Har yanzu a hukumance ba a samu bullar cutar a jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na da ra'ayin cewa hakan ta faru ne saboda ba a gwajin cutar a cikin johohin biyu.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya adadin gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.

Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Talata 19 ga watan Mayu.