Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Wane sabon mataki gwamnatin Najeriya za ta dauka kan dokar kulle a yau?
A yau Litinin 18 ga watan Mayu gwamnatin Najeriya za ta sanar da matakin gaba bayan kammala wa'adin farko na sassauta dokar kulle a ƙasar domin yaƙi da yaɗuwar annobar korona.
To sai dai mai magana da yawun shugaban Najeriya, Femi Adesina ya ce Shugaba Buhari ba zai yi wani jawabi ba dangane matakin da kasar za ta dauka a nan, illa dai gwamnoni su yi aiki tare da Kwamitin Shugaban Kasa Musamman mai yaki da annobar korona wato PTF
Mista Femi ya ce Shugaba Buhari ya riga ya tattauna da gwamnoni dangane da al'amarin ta kafar intanet a ranar Litinin kuma "ya umarci gwamnoni da su bai wa kwamitin hadin kai".
Dama dai babban jami'i a kwamitin, Dr Sani Aliyu ya bayyana ranar Lahadi cewa kwamitinsu ya miƙa wa Buhari shawarwarinsa kuma zai sanar da matakin da za a dauka ranar Litinin.
A rahoton da ta wallafa na daren Lahadi, hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce mutum 5,959 ne suka harbu da cutar korona, 182 sun mutu, sai kuma 1,594 da suka warke.
Mako uku kenan da dage dokar kulle inda aka kakaba dokar hana zirga-zirga a Abuja da kuma jihohin Legas da Ogun da mako guda da zummar daƙile yaduwar annobar korona.
A lokacin da yake bayanin dokar hana zirga-zirgar, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce mazauna garuruwan za su fara fita daga ranar Litinin 4 ga watan Mayu daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na dare.
Har wa yau, daga baya Buhari ya sanya dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin ƙasar, bisa buƙatar ƙungiyar gwamnonin ƙasar.
Duk matakin da Buhari zai ɗauka yana nufin kulawa da lafiyar mutum kusan miliyan 200 na 'yan Najeriya, yayin da wasu da dama ba su san halin da suke ciki ba - ko suna ɗauke da korona ko kuma a'a sakamakon ƙarancin yin gwajin cutar.
Ya zuwa ranar Litinin, mutum 35,345 aka yi wa gwajin cutar a Najeriya.
Tuni jihar Legas ta fito da sabbin tsare-tsare game da dokokin nesa-nesa da juna da ta ce za su yi aiki na tswon mako shida.
Hukumomi a jihar za su riƙa duba masallatai da coci-coci domin ganin shirinsu kafin ba su damar ci gaba da harkokin ibadar.