Coronavirus a Kano: Ƙarin mutum 64 sun kamu a ranar Lahadi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ma'ikatar lafiya ta Kano a Najeriya ta ce an sake samun mutum 64 da suka harbu da korona a rana guda a jihar.

Jadawalin alkaluman da ma'aikatar ta fitar ya ce akwai mutum 111 da suka warke sarai, sannan mamata sakamakon annobar sun kai 36.

Alkaluman daren Lahadi ya zo ne bayan a ranar Asabar ma'aikatar ta ce ba a samu ko mutum guda da ya kamu da cutar ba.

Jihar Kano da ta fi fama da annobar a arewacin Najeriya, yawan masu cutar da wannan sabon adadi yanzu ya kai 825.

Haka kuma an samu karin mutum 18 da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti sakamakon korona a ranar Lahadin, sai karin mutum guda daya mutu.

Jadawalin jiha 34 da birnin Abuja da cutar ta bulla ya nuna Kano ce har yanzu ta biyu a yawan masu cutar korona da mutum 825, a bayan Legas mai mutum 2,550.

Al'ummar Kano dai na dakon ganin ko za a cire musu dokar kulle da wa'adin ke cika ranar Litinin bayan sake tsawaita ta da mako guda.

Tun a makon daya gabata malaman addini a jihar ke ta neman a sassauta dokar musamman don ba da zarafin halartar masallatan Juma'a.

Jihohi kamar Jigawa da Borno sun sanar da dage dokar inda suka bai mutane damar halartar sallolin jam'i, musamman na Juma'a da na sallar idi mai zuwa.

Alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta fitar a daren Lahadi sun nuna cewa yawan masu korona a Katsina sun kai 248, Jigawa na da mutum 201, sai Kaduna mai 142.

Ya zuwa daren Lahadi 16 ga watan Mayu, mutum 5,959 ne suka harbu da korona a daukacin Najeriya, cikinsu, 182 sun rasu sakamakon cutar yayin da 1,594 suka warke kuma aka sallame su.