Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Kano: Karin mutum takwas ne suka kamu da korona ranar Juma'a
Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 883, a cewar ma'aikatar lafiya ta jihar Kano.
Wannan ya biyo bayan samun ƙarin mutum 8 da suka kamu da annobar a ranar Juma'a diin nan.
Sai dai mutum 714 ne ke kwance, bayan an sallami mutum 133 daga cibiyoyin killace masu korona bayan sun warke.
Yawan wadanda suka mutu zuwa yanzu ya tsaya a 36, abin da ke nufin cewa ba a samu ƙarin ko da mutum guda da cutar ta kashe ba daga ranar Talata zuwa ranar Juma'a.
Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar a daren Juma'a ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 3,093.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince ayi sallar Jumma'a da kuma Idi duk da halin da ake ciki, bisa wasu sharudda da gwamnatinsa ta gindaya wa masallatan.
Gwamnatin jihar ta ce za ta dauki masu bayar da agaji 1,500 a masallatan Juma'a da ke jihar domin tabbatar da mutane sun bi shawarwarin da hukumomin lafiya suka bayar domin kaucewa yaduwar cutar korona.
A jihar Jigawa dake makwabtaka da Kano kuwa mutane 16 ne suka kamu a Juma'ar nan, sai mutum 5 a Katsina.
A jihar Borno ma an samu karin mutane 12 da suka harbu, yayin da a Bauchi mutum biyu sun kamu.
Zuwa Alhamis din nan, jimillar mutane 7,261 korona ta kama a Najeriya, yayin da 2,007 suka warke, sai kuma mutum 221 da suka mutu.