Coronavirus a Kano: Mutum 576 suka kamu, 21 suka rasa rayukansu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano a Najeriya ta ce ya zuwa daren Asabar, an samu karin mutum 29 da suka kamu da cutar korona a jihar.

Hakan na nufin adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya kai 576, tun bayan bullar cutar a jihar, sai dai kuma an sallami mutum 32, inda 21 suka rasu.

Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,764 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 343.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa, kuma ci gaba da gwaje-gwaje a jihar bayan an sami tsaiko ya sa aka samu karuwar yawan wadanda ke dauke da cutar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar a daren Asabar na wadanda suka kamu da cutar na nuni da yadda annobar ke kara bazuwa a jihar ta Kano.

A yanzu dai cutar na kara bazuwa a jihohin da ke makwabtaka da Kano - Katsina na da mutum 156 sai Jigawa mai mutum 83, Bauchi na da 161 yayin da Kaduna kuma ta ke da mutum 98.

A cewar sanarwar da hukumar NCDC ta fitar a Twitter, zuwa daren Asabar, mutum 4,151 ne suka kamu a jihohi 34 har da Abuja. Daga cikin adadin, 745 sun warke har ma an sallame su daga asibiti.

Sai dai adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya karu, inda jimilla mutane 128 suka riga mu gidan gaskiya.