Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea za ta dauko Chilwell da Ballo-Toure, Man Utd na zawarcin Salisu
Chelsea ta soma tattaunawa da Leicester a kan Ben Chilwell, mai shekara 23, a yayin da dan wasan na Ingila yake son komawa London. (Express)
Kazalika Chelsea tana son dauko dan wasan bayan Faransa Fode Ballo-Toure, mai shekara 23, daga Monaco a matsayin zabin da ya rage mata idan bata dauko Chilwell ba. (Foot Mercato - in French)
Chelsea, Manchester United da Juventus sun nuna sha'awar sayen dan wasan Fiorentina da Italiya Federico Chiesa, mai shekara 22, wanda za a sayar a kan £60m. (Star)
Manchester United za ta bar golanta mai shekara 23, Dean Henderson, ya ci gaba da zama a Sheffield United a kakar wasan da muke ciki, ko da kuwa ya zarta wa'adin da aka dibar masa na komawa kungiyar daga zaman aron da yake yi. (Manchester Evening News)
Haka kuma Manchester United ta tuntubi Real Valladolid da zummar dauko dan wasan Ghana mai shekara 21, Mohammed Salisu, yayin da kungiyar take son dauko mai tsaron gida a kakar wasa mai zuwa. (ESPN)
Liverpool tana zawarcin Talles Magno, mai shekara 17, daga Vasco da Gama da ke kasarsa ta Brazil,a daidai lokacin da Benfica, Lyon da Sevilla suke rige-rigen sayo dan wasan. (Express via AS)
Dan wasan Juventus dan kasar Bosnia Miralem Pjanic, mai shekara 30, ya amince ya koma Barcelona a kakar wasa mai zuwa. (Gazetta dello Sport)
Barca na ci gaba da shirinta na yunkurin dauko dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, kuma ta nemi Milan ta zabi 'yan wasanta shida, ciki har da dan wasan Faransa mai shekara 26, Samuel Umtiti, a wani bangare na yarjejeniyar. (Sport - in Spanish)
Dan wasan Inter Milan Christian Eriksen, mai shekara 28, ya koma kwana a filin atisayen kungiyar lokacin da aka sanya dokar kulle, saboda dan wasan na Denmark bai samu gida ba tun da ya koma Milan daga Tottenham a watan Janairu. (Sun)
West Ham za ta sayar da dan wasan Ingila mai shekara 21, Nathan Holland, a kan £1m a kakar wasan da muke ciki, a yayin da ake rade radin cewa Sheffield Wednesday tana son dauko shi. (Football Insider)
Arsenal tana son dauko dan wasan Leicester dan kasar Netherlands mai buga gasar Under-19 Dennis Gyamfi, mai shekara 18. (Football Insider)
Hakazalika Arsenal tana son dauko dan wasan Norway mai shekara 19, George Lewis, wanda yanzu ba shi da kwangila, bayan ya taka rawar-gani a kungiyar. (Football London)