Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An rufe majalisar Jihar Nasarawa bayan mutuwar dan majalisa
An rufe majalisar dokokin Jihar Nasarawa bayan wani mamba a majalisar ya rasu sakamakon abin da ake zargin cutar korona ce.
Honorabul Sule Adamu ya rasu ne yayin da ake jiran sakamakon gwajin cutar korona da aka yi masa, inda daga baya gwajin ya tabbatar yana dauke da cutar.
Gwamnan jihar Abdullahi Sule ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar ga manema labarai yayin da yake bayani kan halin da ake ciki game da annobar a jihar.
Gwamnatin Nasarawa ta rufe zauren majalisar tare da killace dukkanin 'yan majalisar da zummar dakile bazuwar cutar a jihar.
Mai taimaka wa gwamman kan harakokin yada labarai ya shaida wa BBC cewa dan majalisar ya nuna alamun cutar kafin a yi masa gwajin.
Ya zuwa daren ranar Asabar, Jihar Nasarawa na da wadanda suka harbu da cutar korona mutum tara, a cewar hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya.