Yau ce ranar 'yan jarida ta duniya

An wallafa

Yau ce ranar 'yan jarida ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin tunawa da irin gudunmuwa da kuma rawar da 'yan jarida ke takawa wajen bayar da labaran abubuwan da ke faruwa a duniya.

An dai kebe kowacce ranar 3 ga watan Mayu na kowacce shekara domin jinjinawa 'yan jarida a duniya.

Taken ranar na bana dai shi ne " Aikin jarida ba tare da tsoro ko Alfarma ba".

To sai dai kuma ranar ta bana ta zowa 'yan jaridar a cikin wani mawuyacin yanayi na annobar cutar korona.

'Yan jarida a fadin duniya na fuskantar kalubale iri-iri a wannan lokaci da kasashen duniya ke yaki da cutar ta korona.

Mannir Dan Ali, dan jarida ne kuma shi ne shugaban kamfanin jaridun Media Trust a Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa, a wannan yanayi na annobar korona da ake ciki a duniya, 'yan jarida na da babbar rawar takawa wajen tabbatar da suna samar da sahihan labarai ga al'umma.

Ya ce ko shakka babu aikin jarida ya kara muhimmanci a wannan lokaci bisa la'akari da yadda kafafan sada zumunta ke taka rawa wajen yada labaran bogi.

Mannir Dan Ali, ya ce " Dole ne 'yan jarida suka rinka yin taka tsan-tsan a wannan lokaci, saboda yadda jama'a musamman ma'abota shafukan sada zumunta ke yada labarai marassa tushe".

Ya ce, yawanci akwai mutanen da su basu yarda cewa akwai wannan cuta ba, to dolene 'yan jarida a nasu bangaren su jajirce wajen ganin sun fahimtar da mutane cewa lallai akwai wannan cuta.

Kazalika ya ce a wannan lokaci 'yan jarida da ma shi kansa aikin jaridar na fuskantar manyan kalubale kamar na labaran bogi, inda jama'a ke yada abin da bai faru ba amma sai su mayar da shi kamar da gaske.

Ya ce to yanzu a wannan yanayi, 'yan jarida dama kafafan yada labarai sun mayar da hankali ne wajen tantance ainihin labaran gaskiya fiye da da.