Boris Johnson ya raɗa wa ɗansa sunayen likitocin da suka duba shi

Carrie Symonds and Boris Johnson

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Boris Johnson da budurwarsa Carrie Symonds sun raɗa wa jaririnsu suna Wilfred Lawrie Nicholas Johnson.

Sunayen na girmamawa ne ga kakaninsu da kuma likitoci biyu da suka kula da Mista Johnson lokacin da yake jinyar cutar korona a asibiti, kamar yadda Mis Symonds ta wallafa a shafinta na Instagram.

Ta gode wa ma'aikatan asibitin Jami'ar Kwalejin Landan da suka kula da ita.

Ta kuma wallafa hotonta da na jaririn da ta haifa a ranar Laraba.

An yi haihuwar ne kwanaki kadan bayan sallamar Firai Ministan daga bangaren kulawa ta musamman a asibiti bayan ya sha fama da cutar korona.

Ms Symonds ta rubuta cewa dan nasu ya ci sunan kakan firai ministan ne, sannan sunan yaron na farkon kuma sunan nata kakan.

Wilfred Johnson dai shi ne kakan firai minista na wajen uba.

Shirin BBC One na ''Who Do You Think You Are'' a shekarar 2008 ya gano cewa an asalin sunan kakan Mista Johnson Osman Wilfred Kemal - amma a lokacin Yakin Duniya Na Farko aka sauta masa sunan mahaifinsa.

Carrie Symonds and her newborn son

Asalin hoton, Carrie Symonds

Bayanan hoto, Carrie Symonds ta godewa ma'aikatan hukumar NHS bayan ta wallafa hotonta da na jaririn a Instagram

Ms Symonds ta kara da cewa sunan jaririn na tsakiyar kuwa wato Nicholas, girmamawa ce ga "Dr Nick Price da Dr Nick Hart - likitoci biyun da suka ceto rayuwar Boris a watan da ya gabata".

Matakin girmama likitocin alamu ne da ke nuna tsananin halin da firai ministan ya shiga a lokacin da yake jinya, a cewar wakilin BBC kan al'amuran siyasa, Jonathan Blake.

Bayan da aka sallame shi daga asibitin, Mr Johnson ya ce da yanzu labari ya sha bamban.

Jaririn shi ne da na farko ga Ms Symonds yayin da Mr Johnson kuwa ke da 'ya'ya biyar.

Sauran 'ya'ya hudun da Mr Johnson ya haifa tare da tsohuwar matarsa Barista Marina Wheeler, duk sun haura shekara 20.

Boris Johnson

Asalin hoton, Andrew Parsons/10 Downing Street

Bayanan hoto, Boris Johnson yakoma Fadar Downing Street bayan haihuwar