Tarihin tauraron fina-finan India, Rishi Kapoor

Rishi Kapoor

Asalin hoton, The federal

An wallafa

Rishi Kapoor jarumi ne da ya yi fice a fina-finan soyayya, dan kabilar Punjabi ne, asalin sunansa Rishi Raj Kapoor, an haife shi a in Chembur, da ke Bombay a ranar 4 ga watan Satumbar 1952, kimanin shekaru 67 ke nan yanzu.

Shi ne da na biyu a wajen Raj Kapoor da mahaifiyarsa Krishna Raj Kapoor, jika ne kuma a wajen Prithviraj Kapoor.

'Yan uwansa da suke ciki daya sune Randhir Kapoor da Rajiv Kapoor da Ritu Nanda da kuma Rima Jain.

Bappaninsa wato kannan mahaifinsa akwai Shashi Kapoor da Shammi Kapoor, sai kuma kawunansa wato kannan mahaifiyarsa sune Prem Nath da Rajendra Nath da Narendra Nath da kuma Prem Chopra.

Rishi dan na gada ne a fim, ma'ana ya gaji fitowa a fim tun daga kakansa.

Fitaccen jarumin ya yi karatu a Campion School, da kuma kwalejin Mayo College.

Rishi ya fara fitowa a fim ne tun yana shekara uku a duniya amma a cikin waka ya fito wato wakar cikin fim din Shree 420 da mahaifinsa ya fito a ciki.

Daga nan bai kara fitowa a fim ba sai a 1970 inda ya fito a fim Mera Naam Joker, fim din mahaifinsa.

Fim din da za a ce Rishi ya fito a matsayin cikakken jarumin fim din shi ne Bobby wanda suka fito tare da jaruma Dimple Kapadia.

Rishi Kapoor

Asalin hoton, Koimoi

Daga nan ne fa ganin irin rawar da ya taka a fim din Bobby sai masu shirya fim suka fara rububin sanya shi a cikin fim.

Wani abu ga jarumin shi ne mafi akasarin fina-finansa duk na soyayya ne, hakan ya sa ake ce masa baban soyayya.

In dai fim na soyayya ne aka sanya Rishi a ciki to abin zai kayatar domin ya iya soyayya sosai.

Don fim din soyayyar nan ma da ya yi tashe wato Laila Majnu Rishi ne ya fito a cikinsa.

Yana daga cikin kyawawan jarumai maza na India, bashi da fitina, gashi mai barkwanci.

Wadannan halaye nasa ne suka sa ya shiga ran mutane da dama ba ma a kasarsu ba har ma a sauran kasashen duniya.

Rishi ya yi fina-finai da dama tare da jarumai da dama ciki kuwa har da Amitabh Bachchan wanda yana daga cikin jaruman India da suka kadu da rasuwarsa.

Bashi da abokin fada,ya samu lambobin yabo da dama sakamakon rawar da ya taka a fina-finai na India ciki har da na gwarzon jarumai.

Kamfanoni da kasashe da dama sun karrama Rishi Kapoor saboda gudunmuwar da ya bayar a fina-finan Bollywood.

Rishi Kapoor da Iyalansa

Asalin hoton, Filmfare.com

Ya auri matarsa Neetu Singh Kapoor a 1980, inda suka haifi 'ya'ya biyu Ranbir Kapoor wanda shi ma jarumi ne a yanzu da kuma Riddhima Kapoor Sahani.

Jarumai da dama sun mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, kamar Akshay Kumar da Ajay Devgan da Shahrukh Khan da Salman Khan da Rajnikant da Jeetandra da Boma Irani da Priyanka Chopra da Kajol da Varun Dhawan da dai sauransu.

Rishi Kapoor ya mutu ne a ranar Alhamis 30 ga watan Afirilu, 2020, bayan ya sha fama da jinya.

Duk da dokar hana fitar da aka sanya a kasar saboda annobar korona, jarumai da dama sun samu damar halartar jana'zarsa.

Jaruman kamar Amitabh Bachchan da dansa Abhishek da Saif Ali Khan da Kareena Kapoor da Aliya Bhatt dai sauransu.

Daga cikin fitattun fina-finanan da ya fito a ciki akwai Karz da Khel Khel mein da Amar Akbar Anthony da Kabhi Khabhe da Yeh Vaada Raha da Chandni da Hum Kisise Kum Naheen da Sargam da Bol Radha Bol da dai sauransu.

Iyalan Kapoor

Asalin hoton, Radio City