Coronavirus ta sa kasuwar Netflix ta bude a duniya

Asalin hoton, Netflix/AFP
Kamfanin Netflix mai samar da manhajar kallon fina-finai ya ga karuwar masu amfani da shi a wannan shekarar, yayin da kasashe da yawa a fadin duniya suka sanya dokar nan ta kulle mutane a gida, kuma mutanen ke neman hanyoyin nishadantar da kansu.
Kusan mutane miliyan 16 ne suka yi rijista da manhajar a watanni ukun farko na shekarar, in ji kamfanin.
Wannan ya kusa ninka yawan mutanen da suka yi rijista da manhajar a watannin karshen shekarar 2019.
Sai dai kamfanin, wanda kan shirya fina-finai na miliyoyin dala, ya ce dokar kulle a fadin duniya ta dakatar da daukar "kusan duka" fina-finai a fadin duniya.
Kuma faduwar farashin kudaden kasashe da yawa na nufin sabbin masu rijista a manhajar da yawa da ke wajen Amurka, inda Netflix yake, ba za su kara wa kamfanin wani abin a zo a gani ba, ba kamar yadda za su kara ba kafin a shiga halin annobar.
Kuma wannan ya yi mummunan tasiri kan kudin da aka samar a duniya gaba daya.
Sai dai duk da haka, darajar kamfanin ya karu da kusan kashi 30 cikin 100 a wannan shekarar, yayin da masu zuba jari ke ganin cewa kamfanin zai iya yi wa mutane amfani a lokacin da suke kulle a gida.


Kamfani mai alamar Damisa
"Netflix shi ne, kuma zai ci gaba da kasancewa kamfanin sadarwar da Covid-19 ba ta yi wa tasiri sosai ba," in ji wani mai sharhi kan kasuwanci a kan intanet Eric Haggstrom.
"Masan'antarsu ta yi dai-dai da al'ummar da suka tsinci kansu da zaman gidan dole."
Bukatar kallon fina-finai a intanet ta yi karuwar da a watan jiya Netflix ya ce zai rage ingancin hotunan bidoyinsa a Tarayyar Turai don rage wa kamfanonin samar da layukan intanet nauyi.
Haka kuma, sai da kamfanin ya dauki karin ma'aikata 2,000 don tallafa wa sauran ma'aikatan kamfanin.
Netflix ya ce mutum miliyan 85 ne suka kalli fim dinsa mai suna Spenser Confidential, tsawon a kalla minti biyu - ma'aunin da yake amfani da shi don ganin alkalumansa.
Haka kuma, an kalli fim dinsa na dogon zango mai suna Tiger King a gidaje miliyan 64.
Rashin Tabbas

Asalin hoton, Netflix
Kamfanin na sa rai zai kara mambobi miliyan 7.5 nan da wata uku zuwa karshen watan Yuni - fiye da yadda masu sharhi ke sa rai.
Amma ya yi gargadin masu zuba jari cewa masu bibiyar manhajar da darajar kamfanin za su ragu idan gwamnatoci suka dage dokar kulle a fadin duniya.
Natflix ya ce yana sa rai ya ci gaba da bin jadawalinsa har zuwa karshen watan Yuni kuma yana ci gaba da mallakar wasu fina-finan da ba shi ya shirya ba don samar wa masu bibiyarsa sabbin fina-finan da za su kalla.
Amma ya ce nan gaba za a fuskanci koma-baya a yawan mutanen da ke kallon sabbin fina-finai.
Paolo Pescatore, mai sharhi a kamfanin PP Foresight, ya ce tsayawa cik da aka yi da shirya finai-finai zai shafi karuwar mutanen da ke kallon fina-finai a intanet a watanni masu zuwa.
"Amma Netflix ba zai fuskanci matsaloli sosai ba saboda yawan fina-finan da ke kansa," a cewarsa.

Sharhi
Daga Zoe Thomas, Wakilin BBC News kan Fasaha

Asalin hoton, Getty Images
Yadda masu rijista da kamfanin Netflix daga farko-farko suka rika karuwa, ya ja hankalin masu zuba jari a Amurka.
Amma karuwar masu amfani da manhajar a lokacin da mafi yawan masu amfani da intanet na duniya ke kulle a gida ba wani abin a yaba ba ne.
Babban abin tambaya shi ne, Netflix zai iya rike wadannan sabbin kwastomomin bayan an dage dokar hana fita ta Covid-19?
Kamfanin na fuskantar karuwar kamfanoni masu gogayya kamar Disney Plus da Amazon Prime, wadanda ke tinkaho da yawan fina-finai don jawo sabbin kwastomomi.
A halin da ake ciki, sabon tsarin kallon fina-finai na Quibi ya kasha biliyoyi don sakin fina-finai da manyan 'yan wasa suka fito a ciki. Kuma a karshen shekarar nan, HBO Max da NBCUniversal za su kaddamar da tsarin Peacock a Amurka.
A duniyar kallo ta shafin intanet, fina-finai su ne mafi muhimmanci kuma karuwar masu gogoya na nufin Netflix zai kara matsa kaimi wajen fitar da fina-finai masu inganci.
A nan ne kuma batun cutar korona ya shigo. Dole Netflix ya dakatar da dauka da shirya sabbin fina-finansa a wannan lokaci.
Abokanan gogoyyarsa ma na fuskantar wannan kalubalen. Amma manyan kamfanoni kamar NBCUniversal da Disney, suna janye shirye-shiryensu da ake kallo sosai, wadanda suka bai wa Netflix aro kuma suna dorawa a mahnajojinsu.

Turai da Gabas Ta Tsakiya da Afrika ne yankunan da mafi yawan sabbin mambobin Netflix miliyan 7 suka fito.
A Amurka da Canada, ba a ga karuwar masu amfani da manhajar ba a shekarun baya amma a baya-bayan nan, mutane miliyan 2.3 ne suka yi rijista da ita, idan aka hada da mutane 550,000 da suka yi rijista a watannin karshe na 2019.
Yanzu kamfanin na da masu amfani da shi sama da miliyan 182 a fadin duniya.
Netflix ya ce kudin shigarsa ya karu da dala biliyan 5.76, wato ya karu da kashi 27 cikin dari, idan aka hada abin da ya samu a shekarar 2019.
Ribarsa ta rubanya daga dala miliyan 344 a watannin farko na 2019 zuwa dala miliyan 709.












