Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wani mutum ya kashe matarsa da wasu mutum 8 a Labanon
Jami'an tsaron kasar Lebanon na ci gaba da neman wani mutum da ake zargin ya kashe matarsa da kuma karin wasu mutum takwas a wani hari mafi muni cikin shekaru da aka shafe ba a samu irinsa ba.
Ana zaton mutumin ya buya ne cikin wani daji da ke kusa da Baakline, wani gari da ke yankin Tsibiran Chouf inda aka yi kisan a ranar Talata, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar ta bayyana.
Rahotannin sun bayyana cewa harin ya rutsa da wasu 'yan Syria biyar, biyu daga cikinsu kananan yara ne.
Har yanzu dai ba a san dalilin wannan harin ba, sai dai wasu majiyoyi a kasar na cewa mutumin da ya kai harin yana da matsalar kwakwalwa.
Maganjin Garin na Baakline ya ce mutumin da ake zargi na fama da tabin hankali.
Firai Minsta Hassan Diab ya yi Allah wadai da wannan mummunan hari, tare da yin kira ga jami'an tsaro da hukumomin shari'a a kasar su hanzarta binciken da suke yi kuma su bayyana ko wane ne wannan mahari.
Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce, a safiyar Laraba masu binciken sun yi amannar cewa abin ya rutsa da dan uwan maharin, saboda tsintar motarsa da aka yi kusa da inda al'amarin ya faru.