Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu coronavirus a Kano sun kai 59, Lagos ba a samu kari ba
Adadin masu cutar korona a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ya kai 59 bayan hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar, ta sanar da karin mutum 23 da suka kamu.
Wannan shi ne adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar a jihar da aka taba sanarwa cikin sa'a 48 sama da mako guda bayan bullar cutar a jihar.
A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa.
Ranar Lahadi ne hukumar NCDC ta bayyana cewa jihar Kano ta mika wani da ya kamu da cutar zuwa mahaifarsa Jigawa bayan da bincike ya gano cewa ya kamu da cutar kobid-19.
Ita ma ma'aikatar lafiya ta jihar a shafinta na Tiwita ta wallafa cewa "zuwa karfe 11:20 na daren Litinin an samu karin mutum 23 da suka kamu da korona kuma har yanzu mutum guda ne ya mutu a jihar.
Har yanzu jihar Kano ce ta uku inda aka fi samun yawan masu fama da cutar baya ga Legas mai mutum 376 da Abuja, babban birnin kasar mai yawan mutane 89.
Gwamnatin jihar tuni ta dauki matakai daban-daban na hana bazuwar cutar kamar rufe kasuwanni da ba da umarnin zama a gida.
A yanzu dai duka jihohin da ke makwabtaka da Kano sun samu bullar cutar - Katsina na da mutum 12 sai Jigawa mai mutum 2, Bauchi na da 7 yayin da Kaduna kuma take da mutum 9.
A cewar sanarwar da hukumar NCDC ta yi a Twitter, mutum 665 ne suka kamu a jihohi 25 har da Abuja. Daga cikin adadin 188 sun warke har ma an sallame su daga asibiti sai mutum 22 da Allah Ya yi musu cikawa.