Coronavirus a Ecuador: Kasar da mutum 5,000 suka mutu a kankanin lokaci

An abandoned corpse wrapped in plastic and covered with cardboard lies on the pavement in Guayaquil, Ecuador, 6 April 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An bar gawarwaki a kan tituna a garin Guayaquil, birni mafi girma a kasar Ecuador
An wallafa

A yankin Guayas, jihar da annobar coronavirus ta fi shafa a Ecuador, lokacin da aka sake tantance alkaluman yawan mutanen da suka mutu, an fahimci wani abu.

Mutum 6,700 sun mutu a makonni biyu na watan Afrilu, Karin mutum 5,000 fiye da yadda aka saba gani duk wata - inda wannan ya sa Guayas ya zama yankin da annobar ta fi yi wa mummunan tasiri a kasar da ma Latin Amurka gaba daya.

Kuma mace-macen ba duka ne na Covid-19 ba: yayin da cibiyoyin lafiya suka durkushe saboda annobar, marasa lafiya da yawa da ke fama da wasu cutukan sun kasa samun kulawar da suke matukar bukata cikin gaggawa.

Guayaquil, garin da ya zama kufai.

"Mun gano gawarwaki a motoci, a motocin daukar marasa lafiya, a gidajensu, a kan tituna," in ji Katty Mejia, wata ma'aikaciyar wurin ajiye gawarwaki a Guayaguil, babban birinin yankin kuma birni mafi girma a Ecuador.

Two women standing next to a closed store in Guayaquil and a covered dead body lying on the sidewalk in the background

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu daga cikin marasa galihu da ba su da matsuguni a birnin suna ta mutuwa a kan tituna

"Dalili daya shi ne ba a kwantar da su a asibiti ba saboda babu gadaje. Idan suka je asibiti mai zaman kansa, dole su biya kudi kuma ba kowa ne zai iya biya ba," a cewarta.

Yayin da cutar korona ta auka wa birnin mai mutane sama da miliyan biyu da rabi, wuraren ajiye gawarwaki sun cika - an rufe da yawa daga cikinsu, yayin da ma'aikata ke tsoron kamuwa da cutar.

A construction worker, building extra niches in a cemetery

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ana ta kokarin samar da filayen da za a mayar makabartu

'Yan uwan marasa lafiya da suka gigice kan bar gawarwakin 'yan uwansu a wajen gidajensu, wasu kuwa sai a bar su a kan gadon da suka mutu tsawon kwanaki ba a dauke su ba.

A halin yanzu, babu sauran sarari a makabartun birnin Guayaquil sai dai a tafi da gawarwaki wasu garuruwan masu makwabtaka a binne su a can.

Tsananin halin da suka shiga a garin, ta kai ana kera akwatin gawa da kwalaye, kuma hatta fursunoni na aikin kera akwatunan gawa da katako.

Mortuary workers carry a coffin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yawan mace-macen ya nunka sau biyar cikin kwana 15 a Guayas

Tattara bayanai

Shugaban Ecuador Lenin Moreno ya ce ya san lallai kasar ta gaza wajen daukar matakan gaggawa dangane da annobar.

Har ya zuwa 16 ga watan Afrilu, gwamnatin ta dage kan cewa lallai mutum 400 ne kawai cutar korona ta kashe a fadin kasar.

Amma bayan da kwamiti na musamman kan cutar koronar ya tattara bayanai, zancen ya sauya.

"Alkalumman da muka samu daga ma'aikatar harkokin cikin gida, da makabartu da rijistar 'yan kasa, mun gano cewa mutum 6,703 ne suka mutu a Guayas kwanaki 15 na farkon watan Afrilu," in ji Jorge Wated, shugaban kwamitin na gwamnati.

"Duk wata mutum 2,000 ne ke mutuwa. Don haka, mun samu karuwar mutum 5,700 da suka mutu fiye da yadda aka saba gani".

People surrounding a coffin on the street

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan ba da jimawa ba za a rasa filin da za a binne gawarwaki a Guayaquil

Ba duka mutanen da suka mutu a lardin Guayas ne cutar korona ta kashe ba - wasu sun mutu ne sanadiyyar ciwon zuciya ko ciwon koda ko wasu cutukan na daban da ke bukatar kulawar gaggawa bayan da suka kasa samun kulawar da ta dace.

Cutar korona ta samu abin da take so a Ecuador.

Wannan lamari ya janyo abubuwa da dama a fadin yankin - shin annobar za ta yi irin wannan tasirin a sauran kasashen Latin Amurka da sauran kasashen duniya da ba su ci gaba ba a bangaren lafiya?

A Wuhan da ke China, ana bitar alkalumman da hukumomi suka fitar, kuma an ga sakamako mai daga hankali.

A Sifaniya, daya daga cikin kasashen da annobar ta fi shafa a Turai, an samu banbanci a yadda aka tattara bayanai sannan aka sanar a matakan jihohi da na kasa.

A man wears a mask while walking in the street on January 22, 2020 in Wuhan, Hubei province, China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mace-macen China sun karu da 1,300, amma sun yi watsi da zargin cewa ba sa boye bayanai

"Bangaren lafiya a Ecuador ya dade da lalacewa. Ya kasance daya daga cikin bangarorin da gwamnatoci da dama suka yi matukar gazawa," kamar yadda Dakta Carlos Mawyin ya shaida wa BBC.

Yana ganin annobar Covid-19 ta samu dai-dai irin wurin da take so a Ecuador.

"Da bangaren lafiya mai rauni da dumbin marasa lafiya, annobar ta sa cibiyoyin bayar da kulawa ta musamman ga marasa lafiya sun durkushe gaba daya," a cewarsa.

Ecuador ta tsawaita dokarta ta hana fita da dare kuma ta yi alkawarin kara yawan gwaje-gwajen marasa lafiya.

Amma ga mutanen Guayaquil da suka ga mutuwar 'yan uwansu, za su iya cewa wannan mataki ya zo a makare.

Línea

(*) Matias Zibell daga Ecuador ya taimaka wajen hada wannan rahoton