A binciki dalilin gobarar sansanin Ngala a Borno — Buhari

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba wa ma'aikatar ayyukan jin kai ta kasar umarnin bincike a kan mutuwar mutum 14 a sansanin 'yan gudun hijra da ke Ngala a jihar Borno.

Gobarar dai ta yi sanadi jikkatar wasu da dama.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar a daren ranar Alhamis 16 ga watan Afrilu, 2020, an kuma umarci ma'aikatar ayyukan jin kan da ta bayar da bayani a kan musabbabin tashin wutar.

Kazalika sanarwar, ta kuma bukaci ma'aikatar da ta bayar da shawarwari a kan hanyoyin da za a bi wajen kaucewa sake afkuwar lamari makamancin wannan.

Shugaban Najeriyar dai ya bayyana gobarar a matsayin abu marar dadi da kuma tashin hankali.

Daga bisani shugaban ya bayar da umarnin kai taimakon gaggawa ga wadanda wannan iftila'i ya shafa, inda ya kuma yi addu'a ga wadanda suka mutu da neman sauki ga wadanda suka jikkata.

Rahotanni dai sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:15 na rana a ranar Alhamis din a sansanin.

Baya ga asarar rayuka, an kiyasta cewa akwai tantunan da 'yan gudun hijirar ke kwana da dama da suka kone.

Ba wannan ne karon farko da aka taba samun gobara a sansanin 'yan gudun hijra a Najeriya ba.

A baya ma dai an taba samun irin haka.