Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An sallami Boris Johnson daga asibiti
An sallami Firaministan Birtaniya daga asibiti bayan ya yi jinyar Covid-19 a dakin kulawar gaggawa a wani asibitin birnin Landan.
An kwantar da Mista Johnson ne a asibitin St Thoma a ranar Lahadin da ta gabata - kwana 10 bayan tabbatar da yana dauke da cutar coronavirus.
Kwana uku Firaministan ya yi a dakin kulawar gaggawa a asibiti kafin ya dawo babban daki a asibitin a ranar Alhamis.
Sai dai Firaministan ba zai koma ofis ba kai tsaye, zai ci gaba da murmurewa a gidansa na Chequers da ke Buckinghamshire, in ji Downing Street.
"Bisa shawarar da likitocinsa suka bayar, Firaiminista ba zai koma aiki nan take ba," kamar yadda wani mai magana da yawun gwamnati ya bayyana a wata sanarwa.
Sanarawar ta ce Mista Johnson ya gode wa ma'aikatan asibitin St Thomas "saboda kyakkyawar kulawar da suka ba shi", ya kuma kara da cewa sauran wadanda suka kamu da cutar ne suka tsaya masa a rai
Yawan mutanen da cutar coronavirus ta kashe a asibiti a Birtaniya sun zarce 10,000 a ranar Lahadi.
Dr Ian Abbs, babban jami'in asibitin Guy's and St Thomas' ya jinjiyawa ma'aikatan asibitin da suka kula da Firaministan sosai, a yayin da kuma suke ci gaba da tabbatar da kulawa ta musamman ga dukkanin marar lafiya.
Budurwar Firaministan, Carrie Symonds, wacce ya rage wata biyu ta haihu, ta fadi a Twitter: "Na gode wa dukkanin wadanda suka aiko da sakwanni na nuna goyon baya."
"Mun kasance cikin wani yanayi a wasu lokuta da muka tsinci kanmu a makon jiya. Zuciyata ta ga duk wadanda ke cikin irin wannan yanayi na damuwa kan masoyansu da ba su da lafiya."
Symonds ta killace kansa bayan ta nuna alamomi na cronavirus amma kuma ba a yi mata gwaji ba.
Sakataren harakokin wajen Birtaniya Dominic Raab ne ke tafiyar da harakokin gwamnati, Ana tunanin Mr Johnson zai dauki tsawon wata daya kafin ya dawo aiki.
Mahaifin Mr Johnson, Stanley Johnson, ya bukaci dansa ya samu lokaci ya murmure sosai.