Ba ma son ganin kowa a kan titunan Daura - Masari

An wallafa

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da sanarwar kulle garin Daura da kewaye ba shiga ba fita, a wani mataki na dakile bazuwar annobar coronavirus, wadda ta addabi duniya.

"Daga safiyar Asabar, ba ma son mu ga kowa a kan titunan garin Daura da kuma kauyukan da ke karkashin karamar hukumar," in ji Gwamna Aminu Masari.

Matakin ya zo ne bayan samun mutum uku da suka kamu da cutar a jihar Katsina, kuma suna da alaka da wani likita da ya rasu bayan sakamakon kamuwa da cutar mai sarke numfashi.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari yayin wani taron manema labarai ranar Juma'a bai bayyana ko tsawon kwana nawa ne matakin na kulle Daura zai dauka ba.

Ya ce: "maganar nan da nake muku yanzu haka ana kan hanyar kawo su Katsina, babban asibiti na tarayya inda ake da cibiyar kebe marasa lafiya, inda za a killace su kuma ana ci gaba da ba su magani.

Gwamna Masari ya ce sun yi shawara da jami'an tsaro da kuma kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da cutar coronavirus na jihar da sauran jami'an lafiya wadanda suka amince a rufe garin Daura.

"Duk garin da ya gwada ko karamar hukumar da ta gwada akwai wannan (cuta), to za mu rufe ta kaf, kamar yadda muka rufe Daura a yau," in ji gwamna.

Ya ce kwamitin kar-ta-kwanan zai tantance kantunan sayar da magani kamar guda uku da kantunan sayar da hatsi uku wadanda mutanen garin Daura za su rika zuwa cefane a lokacin wannan al'amari.

Har wa yau, gwamnatin Katsina za ta tallafa wa mutanen Daura a lokacin da wannan doka za ta yi aiki., a cewar Masari.