Coronavirus: An kai Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson asibiti

An kai Firai Ministan Birtaniya, Boris Johnson, asibiti domin yin gwaji kwana 10 bayan ya kamu da cutar coronavirus, a cewar fadar shugaban.
An kai shi wani asibiti a Landan a daren Lahadi dauke da alamomin cutar ciki har da zafin jiki.
An ce matakin na riga-kafi ne bayan likitansa ya bayar da shawarar yin hakan, amma sakataren harkokin waje ne ake sa ran zai jagoranci wata ganawa kan coronavirus a ranar Litinin.
Editar BBC, Laura Kuenssberg ta ce ana sa ran Mista Johnson zai shafe wani lokaci na daren Lahadi ana yi masa gwaje-gwaje.
Wata sanarwa daga fadar Downing Street ta ce: "Bisa shawarar likitansa, an kai firai minista asibiti a daren yau.
"Wannan matakin na ko-ta-kwana ne yayin da firai minista ke ci gaba da fuskantar alamun cutar kwana 10 bayan ya kamu da ita."
Ta kara da cewa: "Firai ministan ya gode wa ma'aikatan hukumar NHS sakamakon kokarinsu sannan ya shawarci jama'a da su ci gaba da kasancewa a gida domin kare rayuka."
Tun daga ranar 27 ga watan Maris ne Mista Johnson yake aiki daga gida bayan ya kamu da cutar.
Rabon da a gan shi a bainar jama'a tun ranar Alhamis yana tafa wa ma'aikatan NHS daga dakinsa na Downing Street. Sai kuma ganawar da ya jagoranta a ranar Juma'a kan coronavirus.











