Ganduje da mai dakinsa 'ba sa dauke da coronavirus'

Ganduje

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Ganduje ya yi addu'a ga masu dauke da coronavirus
An wallafa

Sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat ya nuna cewa ba sa dauke da cutar, in ji wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar.

Sanarwar, wacce mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar, ya aikewa manema labarai ranar Alhamis ta kara da cewa: "Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki game da wannan sakamako da ya nuna cewa ba sa dauke da cutar.

Za mu ci gaba da addu'ar neman sauki ga dukkan wadanda sakamakonsu ya nuna suna dauke da cutar. Ba tare da la'akari da kasarsu ko kabilarsu da jam'iyyar siyasarsu ko kuma addininsu ba."

Ko da yake sanarwar bata fadi lokacin da aka yi wa gwamnan da mai dakinsa gwajin covid-19 ba, amma ta yi kira ga dukkan al'umma su bi umarnin masana harkokin lafiya wajen wanke hannayensu akai-akai da yin amfani da man goge hannu, wato hand sanitizer da kuma tsaftace muhallinsu.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

"Ku guji zuwa wurin taruwar jama'a musamman kasuwanni da sauran wuraren haduwar jama'a... Zama a gidajenku shi ne ya fi alheri," in ji Gwamna Ganduje.

Gwamnan ya bi sahun wasu gwamnoni, irin su gwamnan Naija, Abubakar Sani Bello; gwamnan Kebbi, Atiku Badugu da sauransu, wadanda suka ce ba sa dauke da cutar bayan gwajin da suka yi.

Sai dai gwamnoni irin su Bala Mohammed na Bauchi, Nasir El-Rufai na Kaduna da Seyi Makinde na Oyo, sun bayyana cewa suna dauke da cutar kuma sun killace kansu inda suke karbar magani.

Karin labarai masu alaka: