Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Jihar Filato za ta rufe iyakokinta ranar Alhamis
Gwamnatin jihar Filato ta ce za ta rufe dukkanin kofofin shiga jihar domin dakile cutar coronavirus daga jihar.
Wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Dan Manjang ya fitar ta ce matakin zai fara aiki ne daga karfe shida na safiyar Alhamis ranar 2 ga Afrilu.
Sanarwar ta ce daga lokacin babu shiga ba fita daga jihar, domin matakin zai ba gwamnati damar tabbatar da matakan dakile cutar coronavirus da ta zama annoba a duniya.
Tuni gwamnatin Filato ta rufe makarantu a fadin jihar.
Cutar dai ba ta bulla ba a jihar Filato, amma mutum uku ya kamu da cutar a makwabciyarta Bauchi inda cutar ta fara kama gwamnan jihar.
Zuwa yanzu jimillar mutum 174 hukumomin lafiya a Najeriya suka ce suna dauke da cutar coronavirus, kuma jihar Legas da Abuja babban birnin Najeriya ne ke da yawan masu dauke da cutar.
Mutum biyu suka mutu sanadiyar cutar, yayin da kuma aka sallami mutum 9.
Karin labaran da za ku so ku karanta