Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An rufe Masallacin Annabi SAW da na Harami
Hukumomi a Saudiyya sun bayar da umarnin rufe Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina da kuma na Harami da ke Makkah saboda fargabar ci gaba da yaduwar coronavirus.
Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar ta ce za a rufe dukkan hanyoyin da ke kai wa ga masallatan biyu.
Kazalika hotunan da gwamnati ta wallafa a shafukan sada zumunta ranar Alhamis da Juma'a sun nuna yadda ake rufe kofofin masallatan da kuma wadanda ke nuna su fayau babu kowa.
Ranar Alhamis gwamnatin kasar ta bayyana cewa an samu karin mutum 36 da suka kamu da coronavirus.
Hukumomin kasar sun ce liman ne kawai za a bari ya yi sallah tare da wasu tsirarun mutane.
Sai dai sun ce ba za a yi sallar Juma'a a masallatan ba.
Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce kawo yanzu mutum 274 suka kamu da cutar jumilla.
Da ma dai tuni aka hana masu zuwa Umrah da aikin Hajji shiga kasar, a wani mataki na hana ci gaba da yaduwar coronavirus.