Maudu'in #RIPTwitter ya shahara yayin da kamfanin ke gwajin sabon tsarin

An wallafa

Twitter na gwajin wani tsari da zai ba da damar sakonnin da ake wallafawa su bace bayan sa'a 24 kamar yadda kamfanin ya sanar ranar Laraba.

Sabon tsarin da ake kira "fleets" a Turance ya na da kamanceceniya da yadda sakonni ke bacewa a manhajojin Snapchat da kuma Instagram.

Sauye-sauyen ya janyo an fara amfani da maudu'in #RIPTwitter yayin da ma'abota shafin suke kokawa cewa sabon tsarin zai sa Twitter ya zama kamar sauran shafukan sada zumunta.

Ya zuwa yanzu dai Twitter na gwajin sabon tsarin ne a Brazil.

Kayvon Beykpour, jami'i a kamfanin ya ce sabon tsarin zai bai wa mutane damar wallafa sakon da suke dari-darin wallafawa don kowa ya gani.

Ya ce sa sako a Twitter kamar "din-din-din ne" wanda zai iya yin barazana ga wasu masu amfani da shafin.

"Muna fatan sabon tsarin zai taimaka wa mutane su wallafa sakonnin da ba za su iya wallafawa a shafinsu ba," kamar yadda ya rubuta a Twitter.

Sakonnin na wucen gadi za su bayyana idan aka danna hoton mai amfani da shafin. Ma'abota shafin ba za su iya danna alamar so ko su fadi wani abun kan sakonnin da za su goge bayan wani lokaci ba.

Ga dai abin da wani ma'abocin shafin ke cewa game da sabon tsarin:

Chris Day ya ce "Babu wanda ya ke son tsare-tsare irin na Facebook. Mutane na son tsarin da zai ba ka damar yin gyara."

Mr Beykpour ya ce tsarin ya yi kamanceceniya da 'Stories' na Facebook da Instagram. Ya ce Twitter za ta banbanta na ta.

Kamfanin dai bai fadi lokacin da za a fara amfani da sabon tsarin ba a duniya.