WHO ta ce a kiyayi labarun karya kan coronavirus a Najeriya

@

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO ta yi gargadin cewa fargabar da ake samu ta sanadiyyar labarun karya game coronavirus a Najeriya na iya kara yaduwar cutar a kasar.

Shugaban ofishin WHO a Najeriya, Dr Peter Clement, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin kasar na bukatar ta hanzarta bayar da sahihan bayanai a kan cutar musamman ga mazauna karkara.

Ya ce ta haka ne jama'a za su san hanyoyin kare kawunansu daga cutar, wadda ya ce na iya yaduwa ta hannun ma'aikatan lafiya marasa kwarewa musamman a cibiyoyin lafiya na 'yan kasuwa da basu damu su fahimci yadda cutar take ba.

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki tare da kamfani Facebook domin takaita yada labarun kanzon kurege kan yaduwar cutar da ta bulla a kasar.

Ministan Yada Labaran kasar Lai Mohammed ya ce Facebook zai rika cire labaran karya ko masu hadari da aka wallafa game da cutar ko yaduwarta a Najeriya.

Don haka ya bukaci 'yan kasar su yi karar bayanan karya game da cutar a kasar da aka wallafa a shafukan zumunta domin a cire su, yana mai cewa masu baza labarun karya na iya amfani da matsalar cutar wurin yada miyagun sakonni.

Hanyoyin kariya daga coronavirus

WHO ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Alamomin cutar coronavirus

Wadanne ne alamomin cutar?

Da alama tana farawa ne daga zazzabi, sannan sai mutum ya soma tari.

Bayan mako guda, mutum zai rika fuskantar yankewar numfashi.

Don haka ya kamata mutum ya je asibiti idan ya fuskanci irin wadannan alamomi.